2025-10-13@15:53:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6881
«Kyanda»:
Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta...
Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga y’in wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta...
Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas (PENGASSAN), ta dakatar da yajin aikin kwanaki uku da ta fara biyo bayan rikici tsakaninta da matatar Dangote. Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Laraba. Hatsarin Jirgin Ruwa: Adadin waɗanda suka rasu ya kai 26 a Kogi Jihar...
“Ina kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya rungumi zaman lafiya, kwanciyar hankali, da haɗin kai a gidajenmu, al’ummominmu, da fadin ƙasarmu. Tare, cikin haɗin kai da ƙauna, za mu iya gina Nijeriya ta mafarkinmu. Barka da ranar ‘Yancin Kai!” in ni Shettima. Akan hakan, Shettima ya jinjinawa ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wanda...
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa ba za su bar irin waɗannan matakai su ɗauke hankalinsu daga manufar tabbatar da zaman lafiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana alhininta game da rasuwar aƙalla mutum 26 waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su. Mutanen sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Ibaji, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Ilushi a Jihar Edo. Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare Gwamna Abba ya bukaci Tinubu...
Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare da kuma takaita zirga-zirgar makiyaya tsakanin kananan hukumomi daga ranar Laraba, daya ga watan Oktoban 2025. Shugaban kwamitin sasanta rikicin manoma da makiyaya na jihar, wanda kuma shi ne kwamishinan Ma’aikatar Noma da Kiwo ta jihar, Dakta Barnabas Malle, ne ya...
‘Yan ƙasashen ƙetare da suka karya dokar shige da fice ta Nijeriya za su fuskanci hukunci, wanda zai iya haɗawa da tara, kora, ko kuma yiwuwar hana sake shigowa Nijeriya nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa aiwatar da yarjeniya ta musamman da kasar china a halin da ake ciki a yankin da kuma yadda duniya take sauyawa da sauri ya zama wajibi ga kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin da yake gabatar...
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, saboda yadda ya siyasantar da aikinsa. Kiran na zuwa ne bayan kwamishinan tare da ilahirin dakarun rundunar a jihar sun kaurace wa halartar bikin tunawa da ranar samun ’yancin kai da aka...
A shekarar da ta gabata, Nijeriya ta ƙuduri aniyar samar da gangar ɗanyen mai 445,000 a kowace rana ga matatar a cikin kuɗin gida (Naira). Jami’an gwamnati sun yi nuni da cewa, shirin, idan ya yi nasara, za a iya fadada shi zuwa sauran matatun mai na masu zaman kansu da ke cikin...
Dakarun sojin Najeriya sun kama wasu mutum biyu da ke sanye da kayan ’yan sanda dauke da motoci biyu kirar Hilux da ke makare da tabar wiwi a jihar Taraba. Dakarun rundunar sojojin ta shida tare da hadin gwiwar jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ne suka sami nasarar cafke mutanen bayan...
Gwamnatin Tarayya ta ce Kungiyar Ma’aikatan Harkokin Man Fetur da Gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta amince da janye yajin aikin da take yi, bayan zaman sulhun kwanaki biyu da aka gudanar tare da shugabannin matatar man Dangote. Zaman sulhun da aka gudanar a ranakun 29 da 30 ga Satumba, 2025, ya gudana ne a karkashin...
Shekara guda bayan shahadar Sayyed Hassan Nasrallah, yanayin siyasa da zamantakewar yankin ya sake yin tasiri da tunawa da shi. Nan da nan kuma shahadarsa ta zama wani muhimmin batu na samun hadin kai a tsakanin kungiyoyi masu adawa da mamaya da kuma sabunta himma ga manufofin tsayin daka. Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa kasar ta shiga sabon salo na gyaran tattalin arziki, kuma matsin da ake ciki na dab da wucewa su zama tarihi. A cikin jawabinsa ga ’yan kasa don bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yancin kai, shugaban ya ce gwamnatinsa ta damu da...
Sama da al’ummomi 100 a karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara sun samu ayyukan raya kasa don kyautata rayuwa ga mazauna. Shugaban zartarwa na karamar hukumar Ifelodun, Alhaji Abdulrasheed Yusuf, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ayyukan gwamnatinsa a cikin shekara daya da ta gabata, yayin da ya...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa ya bayar da umarnin aikewa da jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa dake dauke da makaman Nukiliya da su karaci gabar ruwan kasar Rasha, a matsayin kandagarko. Trump ya kara da cewa; A cikin kwanakin bayan an aiko mana sakon barazana daga Rasha,...
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yaba wa ’yan Najeriya bisa abin da ya kira ‘hakurinsu, juriya da kwazo’ duk da tsananin matsin tattalin arziki da rashin tsaro da suke fama da shi. A cikin sakonsa na murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai da ya aike ga ’yan kasa, Atiku ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun daga ranar 1 ga Oktoba, 1960, Najeriya ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Amma tun daga wannan lokaci, al’ummar Najeriya sun kasance cike da bambance-bambancen addini da kabila da harshe da al’adu da kuma ra’ayin siyasa. Wadannan bambance-bambancen sun kasance ginshiki guda biyu: a wani...
A yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Inda game da rahoton ci gaban Sin na 2025 da cibiyar nazarin samar da ci gaba ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar, Guo ya ce ci gaban Sin mai inganci ya samar da damammaki...
Ɓangarorin biyu sun tashi baran-baran a wata tattaunawar da suka yi ƙarƙashin jagorancin Ministan ƙwadago na Nijeriya, Mohammed Dingyadi a ranar Litinin. Wannan yajin aiki na PENGASSAN ya shafi rufe ɓangarori da dama na harkar mai a Nijeriya, ciki kuwa har da babban kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, tare da dakatar da ba matatar...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinjina wa ’yan Najeriya bisa abin da ya kira “juriya, haƙuri da ƙarfin halin da suke nunawa duk da matsin tattalin arziki da matsalolin tsaro” da ƙasar ke fuskanta. A cikin saƙonsa na taya ’yan Nijeriya murnar zagayowar ranar samun ’yancin kai da ƙasar ta yi shekaru 65...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga daukacin jama’ar kasar Sin da su yi aiki tukuru, tare da ingiza wanzar da zamanantarwa irin ta Sin. Xi, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin Sin, ya yi kiran ne yayin taron bikin cika shekaru 76 da kafuwar...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu sun bayyana alhini kan kisan gillar da aka yi wa Somtochukwu ‘Sommie’ Maduagwu, waata ’yar jarida mai gabatar da labarai a gidan Talabijin na ARISE TV. A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, shugaba Tinubu da uwargidansa sun yi Allah-wadai da kisan, suna...
Xi Jinping da sauran shugabannin sun yi tattaki zuwa gaban ginin, inda ya gyara furannin dake cikin kwandunan. Sannan ya zagaya ginin a wani mataki na nuna girmamawa. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan aiki daya tilo na karamci da adalci ya sake farfado da fatan ma’aikatan jinya da yawa a cikin gwamnatin ku da kuma a cikin ajandar sabunta fata na Shugaban kasa,” in ji sanarwar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Iran zata iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran a yau, kamar irin abubuwan da ta faru a baya, za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali,...
“Wannan muhimmin al’amari ya sake tabbatar da himmar Gwamnatin Tarayya a fili don kiyaye walwala da haƙƙin ’yan fansho dake ƙarƙashin shirin (DBS) bisa ga manufar sabunta fata,” in ji Daraktan PTAD. Mahukunta PTAD sun nuna jin daɗinsu ga shugaba Tinubu kan amincewa da tallafin gaggawar, wanda a cewarsu hakan zai inganta jin daɗi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin soma karɓar haraji daga hannun mata masu zaman kansu waɗanda suka mayar da karuwanci sana’a. Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kuɗi da gyaran dokokin haraji, Taiwo Oyedele, ya ce kuɗaɗen da masu sana’ar karuwanci ke samu za a riƙe cire musu haraji a ƙarƙashin sabuwar dokar haraji ta...
Fadar Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa duk da tana maraba da tsayawa takarar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a Zaɓen 2027, amma ya kwana da sanin cewa har yanzu ’yan ƙasar ba su mance da badaƙalar da aka tafka a lokacin gwamnatinsa ba. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga...
Tsohon Shugaban Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Neja (SUBEB), Alhaji Alhassan Bawa Niworo, ya shiga hannun ’yan bindiga. An yi garkuwa da shi tare da wasu fasinjoji da dama a yammacin Litinin, 29 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 4 na yamma, tsakanin ƙauyukan Felegi da Ibi a kan hanyar Mokwa zuwa New Bussa...
A lokacin, sun yi wa motar ‘yansanda ruwan harsasai yayin da ɗaya daga cikin jami’an ya ji rauni, amma an garzaya da shi asibiti. Ya ƙara da cewa daga baya ‘yan bindigar sun sake tare wata hanya a gaba, inda suka sace fasinjoji a motoci uku. Abiodun, ya ce an tura ƙarin jami’an ‘yansanda tare...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ce kawo yanzu bata samu ba ta samu rubutaccen shirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump kan Gaza ba. Mahmoud Mardawi wani babban jami’in kungiyar ta Hamas ya bayyana cewa har yanzu kungiyar ba ta samu daftarin shirin, wanda kafofin yada labaran Amurka suka wallafa bayanansa. Amma ya...
Jami’an Isra’ila da dama da suka hada da Ministoci masu tsattsauran ra’ayi irin su Itamar Ben-Gvir da Bezalel Smotrich, sun soki Firaminista Benjamin Netanyahu kan neman gafarar Qatar bayan harin da gwamnatin Tel Aviv ta kai kan shugabannin Hamas a kasar a ranar 9 ga watan Satumba. Netanyahu ya nemi uzurin ne a wata ganawa...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya soki Amurka da kasashen Turai nan uku na (E3) kan haifar da koma baya a yarjejeniyar nukiliyar 2015 ta hanyar mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran. Mista Araghchi ya yi wadannan kalamai ne, yayin ganawa da babban sakataren MDD Antonio Guterres, Ya kira sake sanya takunkumin...
Shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina ya sanar da korar daukacin mambobin gwamnatinsa biyo bayan mummunar zanga-zangar da aka shafe kwanaki ana yi a kasar. A wani jawabi da ya yi na tsawon mintuna 17, ranar Litini, , Andry Rajoelina ya sanar da cewa ya ji kiran matasa tare da korar firaministansa da gwamnatinsa. Ya fara...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci jihohin Arewa 19 da su tsaya ƙyam su jajirce su yi magana da murya ɗaya kan harkokin tsaro da tattalin arziki. Gwamnan ya jagoranci taron ranar farko ta bangaren Zuba Jari da Bunƙasa Masana’antu ta Arewacin Nijeriya a ranar Litinin a otel ɗin Abuja Continental. Wata sanarwa da...
Mutanen gari sun kama mutum uku da ake zargin suna da hannu a harin da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Ƙadisau da ke Ƙaramar Hukumar Faskari da ke Jihar Katsina. Al’ummar yankin ne suka kama mutanen suka damƙa su ga jami’an tsaron al’umma na jihar domin gudanar da bincike. Yankin Ƙadisau da kewaye ya sha...
Ƙungiyar manyan ma’aikatan kamfanonin iskar gas da fetur PENGASSAN ta ce tana nan kan bakarta na ci gaba da yajin aiki bayan kasa samun maslaha tsakaninta da matatar Dangote. Bangarorin biyu sun tashi baran-baran a tattaunawar da suka yi karkashin jagorancin ministan kwadago na Najeriya Mohammed Dingyadi a ranar Litinin. A ranar Litinin ne ƙungiyar...
Gwamnatin Tarayya ta sanar da gobe Laraba a matsayin ranar hutu a ƙasar somin bikin cikar ƙasar shekara 65 da samun ƴancin kai. Cikin wata sanarwa da ministan cikin gida na ƙasar, Olibunmi Tunji-Oja ya fitar, ya taya ƴan Najeriya murnar cimma wannan ”babban matsayi”. Ministan ya kuma buƙaci ƴanƙasar su ci gaba da nuna...
Shugaban hukumar kula da fice ta kasa iran frud askari ya bayyana cewa yawan adadin huldar kasuwancin na kasashen waje na kasar iran yana ci gaba da gudana tsakaninta da fiye da kasashen duniya 100. Kuma yawansa ya kai dala biliyan 54.311a cikin wata shidan farko na wannan shakarar. Da yake hira da manema labarai...
Babban mai ba da shawara kan harkokin soji ga Imam Khamenei ya bayar da rahoton cewa, a kalla matukan jirgi 16 na sojojin gwamnatin sahyoniyawan ne aka kashe sakamakon harin makami mai linzami da Iran ta kai a yakin kwanaki 12. Babban mai baiwa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara kan harkokin soji Manjo Janar...
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a fadar White House jiya litinin cewa, yana fatan samun zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya. Trump ya sanar da kaddamar da abin da ya kira “Ka’idojin Zaman Lafiya” a hukumance, tare...
A ranar Talatar nan ake sa ran ci gaba da tattaunawa tsakanin Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur (PENGASSAN) da Kamfanin Matatar Man na Ɗangote kan taƙaddamar da ke tsakaninsu. Ana sa ran za a ci gaba da zaman sulhun, wanda Gwamnatin Tarayya ta kira domin sasanta ɓangarorin ne zuwa da yamma. Hakan ta faru ne...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Abin...
Buƙatun da ASUU ke nema sun haɗa da: sake duba yarjejeniyar 2009 tsakaninsu da gwamnati, samar da ƙarin kuɗaɗen bunƙasa jami’o’i, biyan bashin albashin da suke bi, da samar da ingantaccen tsarin kuɗi mai ɗorewa ga jami’o’i. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ba wa Gwamnatin ƙasar Qatar haƙuri kan harin da ƙasarsa ta kai a birnin Doha, wanda ya yi ajalin wani jami’in tsaron Qatar. Netanyahu ya bayar da haƙuri ne a yayin wata tattaunawa da shugaban Amurka, Donald Trump ya shirya tsakaninsu da Fira Ministan Qatar, Mohammed Al-Thani. A saƙon...
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nemi afuwar firaministan Qatar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani a ranar Litinin din nan kan harin da jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka kai kan Qatar a baya-bayan nan wanda ya yi sanadin mutuwar wani jami’in tsaron Qatar, kamar yadda wata majiya mai tushe ta shaida wa Axios. An bayar...