Majiyar Gwamnatin Yamen Ta Ce HKI Ta Kai Wasu Sabbin Hare-Hare Kan Kasar
Published: 10th, September 2025 GMT
Jiragen yakin HKI sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a yau Laraba, inji tashar talabijin ta Al-Masirah na gwamnatin kasar.
Labarin ya kara da cewa yahudawan sun kai hare-haren ne a tsakanin wasu duwatsu a cikin kasar, da kuma kan cibiyar kungiyar Ansarullah da ke tsakiyar birnin San’a babban birnin kasar, da kuma ma’aikatar tsaron kasar.
Wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyanawa kamfanin dillancin labaran reuters kan cewa yahudawan sun kai hare-haren kan wani barikin soja ne a yau Laraba.
Kafin haka dai sojojin Yemen sun kai kaiwa HKI hare-hare a gewayen birnin Qudus da kuma tashar jiragen saman da Ramona da ke kudancin kasar kusa da birnin Ummu Rashrash ko Ilaat kamar yadda yahudawan suke kiransa.
Gwamnatin kasar Yemen dai ta shiga yaki da HKI ne tun watan Octoban shekara ta 2023 tare da manufar tallafawa Falasdinawa a Gaza wadanda HKI takewa kissan kiyashin kusan shekaru biyu Kenan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Aragchi: Yarjeniya Da IAEA Ya Nuna Hakurin Iran Bayan Hare-Hare Kan Cibiyoyin Nukliyarta September 10, 2025 Iran Ta Bukaci Kasashen Musulmi Su Dauki Mataki Guda kan HKI bayan Harin Qatar September 10, 2025 Sojojin HKI Sun Ragargaza Hasumiyyar Tayyib II A Kokarin Korar Falasdinawa Daga Birnin Gaza September 10, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan Al-Mujtaba (a) 138 September 10, 2025 Araqchi Ya Isa Kasar Tunisiya A Wata Ziyarar Aiki Da Ya Kai. September 10, 2025 Babu Gaggawa Na Fara cire Haraji Kashi 5 Na Man Fetur A Nijeriya September 10, 2025 Da Alama Nijeriya Ta Rasa Tikitin Kai Tsaye Na Zuwa Gasar Kofin Duniya September 10, 2025 Iran Da Hukumar IAEA Sun Fahimci Juna Kan Shirinta Na Nukiliya . September 10, 2025 Harin Isra’ila A Qatar ya kalubalanci Grantin Tsaron Amurka September 10, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Bayar Da Izinin Aikewa Da Wani Kaso Na Khumusi Ga Falasdinawa September 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA