Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Yaya Da Ƙannuwa Da Wasu A Zaria
Published: 10th, September 2025 GMT
Yayin da aka gano gawar Surajo a ranar Litinin, an gano gawar Fatima washegari, Talata. Sai dai har yanzu ba a gano gawar kanwar Fatima ‘yar shekara uku, Haneefa ba.
A lokacin da lamarin ya faru, Fatima tana goye da kanwarta Haneefa mai shekaru uku a duniya.
Su biyun suna dawowa ne daga gidan kakarsu da ke Magume zuwa gidan su da ke Tudun Jukun.
Malamin Islamiyyar su Fatima, mai suna Malam Daddy ne ya yi musu rakiyar hanya acikin kekensa mai taya Uku (Keke-napep).
Shaidun gani da ido sun ce, abin takaicin ya afku ne a mahadar da ke kusa da Cocin Nasara Baptist da ke kan hanyar Gaskiya babban layi a Tudun Jukun.
Sun ce yayin da direban keken, Malam Daddy ya tsallake rijiya da baya, amma Fatima da karamar kanwarta, Haneefa ruwan ya tafi da su.
Shaidan ya ci gaba da cewa, wani mutum da ya garzaya wurin don ya cet su, shi ma ruwan ya tafi da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wani ɗan ƙasar Indiya tare da wasu mutane uku bisa zargin shigo da ƙwayoyin Tramadol da aka ƙiyasta darajarsu ta kai naira biliyan uku (N3bn) zuwa cikin ƙasar.
A cewar NDLEA, wannan shi ne kamen ƙwayoyi mafi girma da hukumar ta yi a cikin shekarar nan, lamarin da ke nuna yadda safarar miyagun ƙwayoyi ke ƙaruwa a ƙasar.
Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a NijarCikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa jami’anta sun kama mutanen ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, bayan sun samu bayanan sirri da suka taimaka wajen gano su.
NDLEA ta bayyana cewa ƙwayoyin Tramadol ɗin da aka gano an shigo da su ne cikin kwalaye a matsayin maganin multivitamins, yayin da ake ƙoƙarin fitar da su daga filin jirgin a wasu manyan motoci.
“Ƙwayoyin da aka kama ba su da wata alaƙa da amfani na lafiya, waɗanda aka shigo da su a ɓoye a matsayin maganin rage kasala da ƙara kuzari (multivitamins),” in ji sanarwar NDLEA.
Rahotanni sun nuna cewa a da likitoci na bayar da Tramadol ne don rage zafi da raɗaɗin ciwo, amma yanzu ta zamo annoba musamman a tsakanin matasa, wadda ke haddasa mummunan maye da illa ga lafiya.
Hukumar ta nuna damuwa game da yadda yawan masu amfani da Tramadol ke ƙaruwa ba wai a Najeriya kaɗai ba, har ma a wasu ƙasashen Afirka, duk da illolin da ƙwayar ke haddasawa, kamar matsalolin taɓin hankali ko ma rasa rai gaba ɗaya.