Dawowa Hutu Ya Tayar Da Hankalin Iyaye Saboda Ƙarin Kuɗin Makaranta
Published: 14th, September 2025 GMT
Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki.
“Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin makaranta, su ƙara wasu sabbin abubuwa, kamar su kuɗin ICT, wasanni tsaro.
A makarantar( Prime School ) da ke, Karu,inda aka ƙiyasta ana biyan kusan Naira 300, 000, kowane zangon karatu,wani Malamin da baya son a ambaci sunansa ya ce, akwai ƙarin kuɗin makaranta waɗanda suna da alaƙa ne da lamarin daya shafi kayn zuwa makaranta, bunƙasar makaranta, da kuma sauran abubuwa.
“Idan aka dukkan ƙarurrukan da aka yi abin zai zama da akwai ɗaure kai. Kuɗin haya ya ƙaru a wannan unguwa idan kuma mutum ya yi bincike kuma za a gane irin mutanen da suke zama a wurin, waɗanda abinda suke samu ba kasafai yake biya masu buƙata ba. Don haka idan har ka sa ɗanka wannan makaranta,duk da yake dai z aka, iya biya,amma idan wani babban abu ya taso kamar kiuɗin haya abin sai dai ayi shiru kamar yadda ya ce,”.
Wani mahaifi, Joseph Hange wanda ‘yarsa take zuwa makarantar Bright Child Academy, Lugbe, cewa ya yi sabuwar shekarar karatun ta zo da abubuwa masu sosai zuciya.
“Abin bai tsaya kan maganar ƙare-ƙaren kuɗaɗen bane kawai na kuɗin makaranta, abinci, Littattafai, suturar zuwa makaranta, ziyarar buɗe ido, duk a haɗa su wuri ɗaya. Kamar su da suke harkar kasuwanci, lamarin tattalin arzikin ba shi da daɗi.Cewa ya yi sun tattauna a gida ko daga ƙarshe irin wannan tafiyar za ta ɗore”.
Yayin da Iyaye lamarin ya hana su kwanciyar hankali,su ma Malaman makarantar kamar duk jirgi ɗaya ya ɗauko su.Domin kuwa yawancin makarantu yawan ƙarin kuɗin makaranta bai kai wag a ƙarin albashi ga su Malaman makarantar.
Wani Malami mai suna Moses Sachi a Abuja shi ma abin ya dame shi, saboda kuwa cewa yayi “Muna dai jin Iyaye suna kokawa, amma mu ma a matsayinmu na Malamai, matsalar da take damun Iyayen yaran muma ita ce ke damun mu .Lamarin kuɗin haya, abinci, da zirga- zirga abin yana ci mana tuwo a ƙwarya.
Wasu daga cikinmu akwai ayyukan da muke yi domin a samu tsira da mutunci kamar, zuwa koyar da darussa a gida, ƙananan sana’oi, kawai saboda dai mu samu kulawa da Iyali . Wasu makarantu sun ɗan yi ƙarin albashi wanda bai maganin matsin tattalin arzikin da kowa yake fuskanta ba, bama kamar talaka kamar yadda ya jaddada” .
Binciken da LEADERSHIP ta yi rahoton ya nuna matslar ba kawai ta ƙare bane kan ƙarin kuɗin makaranta ba.Kuɗaɗen haya sun ƙaru a sassa daban daban kamar su Abuja, Legas, da kuma wasu manyan wurare kamar Karu, Lugbe, da Gwarimpa da sauarn sassan Babban Birnin Tarayya Abuja, masu gidaje sun ƙara kuɗin haya da kashi 30 kamar yadda binciken ya nuna
Shi yasa Iyayen da suke biyan kuɗin makaranta dubban Nairori yanzu dole ne su san irin hanyar da za su bi, domin su nemi ƙarin kuɗin da za su cika domin biyan haya.
Wani mahaifi a Nyanya, mai suna Isaac Terseer, ya yi lamarin kallon abinda zai yi wuyar jurewa:
Inda ya ce “Wannan tamkar mutum ya riƙa bin inuwa ne da ƙoƙarin kamata.An ƙara kuɗin makaranta, kuɗin haya sun ƙaru.
Wannan halin ƙuncin rayuwa tana sa mutane ko iyalai su cikin halin ni’yasu kan yadda za su yanke shawarar daga cikin abubuwan da suka kamata su yi su ɗauki ɗaya da suke ma kallpon ya fi muhimmanci. Wasu na canza wa ‘ya’yansu makaranta zuwa wadda kuɗin da za su iya biya.Wasu suna tunanin yanke shawarar a riƙa koya masu a gida, ko kuma maida su makarantun gwamnati duk kuwa da yake akwai matsalar kayan aiki da, da rashin nagartar koyarwar.
An samu bayanan da suke nuna Iyaye na biyan tsakanin Naira milyan 3 zuwa 5 kowane zangon karatu.
Ta ɓangaren tsaka- tsaki ana biyan Naiar 800,000 zuwa milyan 2.5 kowane zangon karatu.
Waɗanda ake ma kallon masu sassauci ne a Abuja ana biyan Naira 120,000 zuwa 200, 000 a kowane zangon karatu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Makaranta kowane zangon karatu kuɗin makaranta zuwa makaranta ƙarin kuɗin kamar yadda kuɗin haya
এছাড়াও পড়ুন:
Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta naɗa Luciano Spalletti a matsayin sabon kociya bayan sallamar Igor Tudor da ta yi a farkon makon nan.
Juventus ta ƙulla yarjejeniya da tsohon kociyan na Inter Milan da Roma da Udinese da Zenit St Petersburg da kuma tawagar ƙasar Italiya, har zuwa ƙarshen wannan kakar, yayin da take fatan samu gurbin zuwa gasar Kofin Zakarun Turai ta Champions League ta baɗi.
Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – ZulumSpalletti, shi ne kociyan da ya jagoranci Napoli wajen lashe gasar Serie A a 2023, wadda ita ce karon farko cikin shekaru 33, inda a yanzu ake fatan zai ƙara daidaita Juventus da ke fama da rashin katabus da matsalolin kuɗi tun daga 2022.
Spalletti, wanda aka sani da ƙwarewa wajen gina ƙungiya mai ƙarfi, ya dawo horaswa bayan gazawar da ya yi a matsayin kociyan Italiya a gasar Euro 2024, da kuma shan kashi a hannun Norway yayin wasan farko na neman tikitin Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Zuwa yanzu dai Juventus tana matsayi na bakwai a gasar Serie A da tazarar maki shida tsakaninta da Napoli da ke saman tebur, inda wasan farko da Spalletti mai shekaru 66 zai ja ragama shi ne da Cremonese.