Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina
Published: 13th, September 2025 GMT
Wani mahaifi, Mande Achagh, ya ce matsalar ta fi yin ƙamari a gundumarsa ta Agagbe, a ƙaramar hukumar Gwer West inda yawancin waɗanda basu da matsuguni suka samu mafaka, a wurare na musamman, makarantu, da kuma wasu gundumomi na al’umma.
“Matsalar tafi matuƙar lalacewa a Gwer ta Yamma abin kuma ya shafi makarantu sosai.
“Irin matsalar da su yaran namu suke fuskanta dangane da karatunsu ba abinda za ayi wa riƙon sakainar kashi bane. Abin yana matauƙara ɓata mani rai, saboda wasu wuraren yara suna karatu ne a ƙarƙashin itatuwa, yayin da wasu kum asuka daina zuwa makaranta gaba ɗaya kamar yadda Achagh ya ce”.
Ga Jacintha Terhemen, wadda ita ɗalibi ce ‘yar makarantar Sakandare a wani harin ta’addanci da aka kai a Yelwata, ƙarƙashin ƙaramar hukumar Guma, cewa tayi duk da yake, makarantar da take abin bai shafe ta,ba saboda babu mutanen da suke kwana, amma, a, makarantun Firamare ana amfani ne, da su tare da mutanen da ta’addancin ƴan ta’adda ya raba su da garuruwan su.
“A sansanonin Ugba a Logo da Ortese a Guma, ana zuwa makaranta yayin da suma ƴan gudun Hijirar suna nan. Gwamnatin Jihar Benuwe ta ƙaddamar da wani tsari na samar da wuraren kwana masu inganci, amma hanya da za abi ita ce take da wahala sai an sa haƙuri.
An riga an sa tsari, gwamnati kuma tana neman taimako daga majalisar ɗinkin duniya da kuma Tarayyar Turai da sauran abokan tafiya masu taimakawa daga waje domin a aiwatar da shi tsarin. Aikin ana sa ran zai ci Naira Tiriliyan ɗaya, don haka abin yana buƙatar kuɗi da yawa ya kuma ƙunshi dukkan abubuwan more rayuwa waɗanda daga ƙarshe za su kawo ƙarshen matsalolin da ake fuskanta.
Neja
Makarantun da ake amfani da su a Jihar Neja wajen matsugunnin ƴan gudun Hijira sun haɗa da Central Firmare, Gwada; Central Firamare School, Kuta and Central Firamare, Erena, dukkansu a ƙaramar hukumar Shiroro.
Ɗaya daga mutanen da suka rasa matsuguni, Ahmed Almustapha, da yake sansanin Kuta, ya shaidawa Jaridar ƙarshen mako cewa wasu daga cikin yaran an maida su zuwa Model Firamare yayin da ƴan azuzuwa ne aka bar ma, sha’anin da ya shafi karatu a Central Firamare.
“Ba duka azuzuwa bane, ƴan gudun hijirar suke amfani da su ba. Wasu azuzuwan har yanzu ana amfani da su ne wajen yin karatun yara a makaranta, amma wasu Iyaye sun cire ‘ya’ansu daga Central Firamare,wurin da, ƴan gudun hijira suke zama, suka sasu a makarantar Model, Firamare.’Ya’yan mutanen da ta’addanci ya rutsa da sune kawai basu zuwa makaranta yanzu.
Wasu malaman da suke koyarwa ƴan sa kai su kan zo su koyar da su, amma yanzu sun bar zuwa.Bamu san dalilin da yasa ba,”.
Da yake makarantun da abin ya shfa ƴan gudun Hijira ne suke kwana, yawancin ƴan makarantar, an tilasta masu ne su koma wata makarantar, ko gaba ɗaya ma su bar zuwan. Wannan halin ba wai lamarin karatu kaɗai ya shafa ba,ƴan makaranta da Malamai, har ma ya maida wasu abubuwan da ake amfani, da su, sun lalace, hakan yasa cikin makarantar bai da wata sha’awar kallo . Shugaban makarantar Central Firamare, Kuta, Ya’u Ibrahim ya ce an bar shi da azuzuwa 9 kaɗai bayan kuma ga yawan ƴan makaranta da ya kai 1,360, inda yace sauran azuzuwan ƴan gudun hijira ne suke zama.
Ibrahim ya nuna rashin jin daɗinsa akan irin halayen su ƴan gudub hijirar, musamman ma yadda suke yin kashi a fili wanda yin hakan ba ƙaramar matsalar da take shafar lafiya bace, ga su Malamai, da kuma ƴan makaranta.
“Maganar gaskiya kasancewar ’yan gudun hijira ba ƙaramar matsala bace ga lamarin daya shafi lafiya gare mu. Suna kashi duk inda suka ga dama cikin makaranta, yanzu ko ina wari yaje yi.
“Yaran da su ma basu da matsuguni ba a sa su, makaranta ta, ba; ban san ko wane dalili bane ya sa. Babu waniɗan makarantarmu da ya bari saboda akwai ƴan gudun hijira a makarantarmu. Babbar matsalar da muke fuskanta ita ce rashin isassun azuzuwa saboda sai da muka raba ƴan makarantar uku, wato kowace rana da akwai waɗanda za su zo saboda yawansu ana kuma son a kauce ma cunkoso. Ga kuma irin yadda ake zama a sansanin wani abin damuwa ne shi ma kamar yadda ya ƙara jaddadawa”.
Katsina
An lura da cewa a Jihar Katsina da akwai yara waɗanda basu zuwa makaranta su kuma ne ke ta gararanba kan titunan manyan garuruwa a faɗin Jihar saboda lamarin da ya shafi ta’addanci da sauran laifuka. Da yake basu da wani wuri takamimi da aka ware masu domin su zauna a duk faɗin Jihar, yawanci suna zama ne da danginsu waɗanda suke a manyan garuruwa,ya yin da wasu suke zuwa makarantu ko wasu gine- gine ma mutane,irin hakan ko shakka babu yna shafar ilkimin yara a wasu makarantu.
Bada daɗewa bane mutanen da suka rasa matsugunin su daga wurare 12 daga ƙananan hukumomin Bakorı da Faskari waɗanda aka tilasta ma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ƴan gudun hijira Central Firamare ƴan makaranta zuwa makaranta a makaranta
এছাড়াও পড়ুন:
An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
Antoni Janar na Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke birnin Yamai a Nijar, ya bayyana cewa an kama tsohon Ministan Harkokin Waje, Ibrahim Yacoubou, bisa zargin hannunsa a cikin wata aika-aika ta kisan kai domin yin tsafi.
A cewar Maazou Oumarou, lamarin ya samo asali ne daga wani binciken ’yan sanda da aka fara gudanarwa tun a ranar 29 ga Yuli, 2025.
KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan NejaYa bayyana cewa, an soma gudanar da binciken ne dangane da yunƙurin kisa a wani yanki da ke wajen birnin Yamai, lamarin da ya kai ga cafke ababen zargin a garin Dosso.
Wani mutum mai suna Mahamadou Noura ne ya bayyana cewa shi ne ya yi yunƙurin kisan, tare da wasu kashe-kashe guda shida da ya aiwatar a baya, bisa umarnin wasu mutane, ciki har da tsohon ministan Ibrahim Yacoubou.
Mutumin ya shaida wa mahukunta cewa ya aikata hakan ne domin yin tsafi da gawarwakin, a madadin wasu mutane da suka haɗa da: Issa Ali Maiga da Ismael Morou Karama da Elhadji Bilya da kuma Issa Seybou Hama.
TRT ya ruwaito cewa tuni dai an cafke duk ababen zargin, yayin da Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta umurci ’yan sanda da su ci gaba da bincike tare da ɗaukar ƙarin matakan da za su tabbatar da gaskiya.
Sanarwar ta ce: “Manufar wannan mataki na shari’a ita ce a tattara cikakken rahoto da ke ƙunshe da dukkan abubuwan da suka faru, sannan a miƙa shi ga ɓangaren gurfanarwa.”
Mai shigar da ƙara a ɓangaren gwamnati ya ce, la’akari da girman wannan lamari, wajibi ne a gudanar da bincike cikin gaggawa.
Haka kuma ya buƙaci al’umma da su mutunta ’yancin kotu tare da bayar da cikakken goyon baya domin fayyace gaskiya.
Ana iya tuna cewa, Ibrahim Yacoubou na daga cikin manyan jami’an da aka kama bayan juyin mulkin Nijar na ranar 26 ga Yuli, 2023, sai dai daga bisani an ba shi beli na wucin gadi a cikin watannin baya.