An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
Published: 15th, September 2025 GMT
Antoni Janar na Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke birnin Yamai a Nijar, ya bayyana cewa an kama tsohon Ministan Harkokin Waje, Ibrahim Yacoubou, bisa zargin hannunsa a cikin wata aika-aika ta kisan kai domin yin tsafi.
A cewar Maazou Oumarou, lamarin ya samo asali ne daga wani binciken ’yan sanda da aka fara gudanarwa tun a ranar 29 ga Yuli, 2025.
Ya bayyana cewa, an soma gudanar da binciken ne dangane da yunƙurin kisa a wani yanki da ke wajen birnin Yamai, lamarin da ya kai ga cafke ababen zargin a garin Dosso.
Wani mutum mai suna Mahamadou Noura ne ya bayyana cewa shi ne ya yi yunƙurin kisan, tare da wasu kashe-kashe guda shida da ya aiwatar a baya, bisa umarnin wasu mutane, ciki har da tsohon ministan Ibrahim Yacoubou.
Mutumin ya shaida wa mahukunta cewa ya aikata hakan ne domin yin tsafi da gawarwakin, a madadin wasu mutane da suka haɗa da: Issa Ali Maiga da Ismael Morou Karama da Elhadji Bilya da kuma Issa Seybou Hama.
TRT ya ruwaito cewa tuni dai an cafke duk ababen zargin, yayin da Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta umurci ’yan sanda da su ci gaba da bincike tare da ɗaukar ƙarin matakan da za su tabbatar da gaskiya.
Sanarwar ta ce: “Manufar wannan mataki na shari’a ita ce a tattara cikakken rahoto da ke ƙunshe da dukkan abubuwan da suka faru, sannan a miƙa shi ga ɓangaren gurfanarwa.”
Mai shigar da ƙara a ɓangaren gwamnati ya ce, la’akari da girman wannan lamari, wajibi ne a gudanar da bincike cikin gaggawa.
Haka kuma ya buƙaci al’umma da su mutunta ’yancin kotu tare da bayar da cikakken goyon baya domin fayyace gaskiya.
Ana iya tuna cewa, Ibrahim Yacoubou na daga cikin manyan jami’an da aka kama bayan juyin mulkin Nijar na ranar 26 ga Yuli, 2023, sai dai daga bisani an ba shi beli na wucin gadi a cikin watannin baya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ibrahim Yacoubou Nijar
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu.
Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina makarantu kawai ba, yana ta’allaka ne ga ingancin malamai, kayan koyarwa da kuma yanayin makarantu.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara ɗaukar malamai tare da horas da su akai-akai domin rage cunkoson ɗalibai da malamai da kuma horar da su sabbin dabarun koyarwa.
“Wannan shiri ɗaya ne daga cikin mafi kyawu da muka gani. Idan wani ya yi kuskure, sai a hukunta shi, yayin da duk wanda ya yi fice, wajibi ne a yaba masa. Wannan shi ne yadda ake samun cigaba,” in ji gwamnan.
Ya bukaci sauran hukumomin ilimi kamar Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare, Hukumar Ilimin Addinin Musulunci, da Ma’aikatar Ilimin Firamare su yi koyi da wannan tsari domin ƙara ƙarfafa gwanintar malamai a dukkan matakai.
Gwamnan ya kuma sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da maida hankali wajen gina makarantu, horar da malamai, da walwalar su.
Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da baiwa bangaren ilimi goyon baya don inganta sakamakon koyo a makarantu a fadin Jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria