Yadda zanga-zangar matasa ta rikiɗe zuwa tarzoma a Nepal
Published: 11th, September 2025 GMT
Zanga-zangar matasa a Nepal, da aka ƙirƙira a matsayin “Gen Z Revolution,” ta ɓarke ne da nufin ƙalubalantar rashawa da takunkumin amfani da kafofin sada zumunta, sai dai ta rikiɗe zuwa tarzoma mai muni.
Rahotanni sun bayyana cewa, an fara zanga‑zangar ne sakamakon hana amfani da manyan kafafen sada zumunta guda 26, ciki har da Facebook, X da YouTube, lamarin da ya fusata matasa sosai.
An dai soma zanga‑zangar cikin lumana, amma gwamnatin ta ƙasar ta yi ƙoƙarin daƙile muryar matasan, wanda ya sanya masu zanga‑zangar da dama suka riƙa taruwa a Maitighar Mandala — suka mamaye hanyar shiga Majalisar Ƙasa.
An ƙona matar tsohon firaministan NepalRabi Laxmi Chitrakar, matar tsohon Firaministan Nepal, Jhalanath Khanal, na daga cikin wadanda tarzomar ta rutsa da su, ina aka bayyana rasuwarta bayan masu zanga-zanga sun banka wa gidansu wuta a unguwar Dallu da ke birnin Kathmandu a ranar Talata.
Bayanai sun ce masu zanga-zanga a ƙasar mai tsaunuka da ke fama da tashin hankali mafi muni cikin shekaru da dama sun tarfa matar tsohon firaministan ne a cikin gida kafin su kunna wutar.
An harbe ’yan sanda 3 har lahira a Kogi An harbe ’yan sanda 3 har lahira a KogiAn garzaya da ita asibitin kula da waɗanda ibtila’in ƙuna ya afkawa da ke Kirtipur cikin mummunan yanayi, amma daga ƙarshe ta ce ga garinku nan sakamakon munanan raunuka da ta samu.
Rasuwarta ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar matasa a duk faɗin Nepal tsawon kwana biyu, duk da cewa gwamnati ta ɗage takunkumin da ta saka kan kafafen sada zumunta a farkon makon nan.
Masu zanga-zangar na neman jami’an gwamnati sauka daga kujeru saboda zargin cin hanci da rashawa, nuna son kai a siyasa da kuma taɓaɓarewar tattalin arziki.
Tun dai daga ranar Litinin aka fara tashin hankali, kuma rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutum 22 sun mutu yayin da sama da 300 suka ji rauni.
Kungiyar Amnesty International ta zargi ’yan sanda da amfani da harsasai wajen tarwatsa masu zanga-zangar.
Bidiyoyin da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ake jefa bama-bamai da aka haɗa da man fetur a gidajen fitattun ’yan siyasa, ciki har da na tsofaffin Firaministoci — K.P. Sharma Oli, Sher Bahadur Deuba, da kuma Pushpa Kamal Dahal.
Muhimman gine-ginen gwamnati, ciki har da Singha Durbar (hedikwatar gwamnati) da fadar shugaban ƙasa, Sheetal Niwas, su ma an kai musu hari.
A yayin da tashin hankali ke ƙara tsananta ne Firaminista K.P Sharma Oli mai shekaru 73, ya miƙa takardar murabus ga shugaban ƙasa a ranar Talata, yana mai cewa matakin “na da muhimmanci don ɗaukar matakan samun mafita a siyasar ƙasar.”
Haka kuma, wasu ministocin gwamnati da suka haɗa da na ruwa, noma da cikin gida, sun yi murabus, domin nuna adawa da yadda tarzomar ke ƙara tsananta.
Yanzu haka dai ƙasar ta faɗa cikin wani yanayi na fargaba a yayin da hukumomi ke ƙoƙarin dawo da doka da oda, inda ake ta kira da a koma kan teburin tattaunawa domin kawo ƙarshen rikicin.
A yayin da sojoji suka ayyana dokar hana fita tare da gudanar da sintiri a birnin Kathmandu, matasan Nepal da suka gudanar da zanga-zangar da sunan adawa da cin hanci da rashawa sun yi iƙirarin cewa wasu masu neman dama ne suka ƙwace zanga-zangar wadda ta rikiɗe ta zuwa tashin hankali.
Zangar-zangar da kuma soma ta lumana ce — MatasaƘungiyoyin matasa sun nesanta kansu daga ɓarnar, suna masu cewa masu son yin amfani da dama ne suka shiga suka lalata zanga-zangar.
Sojojin da suka kafa dokar hana fita a faɗin ƙasa har zuwa safiyar Alhamis, sun yi gargaɗin hukunta duk wanda aka samu da hannu a tashin hankali ko ɓarna.
Rahotanni sun ce an kama mutum 27 da ake zargi da hannu a fashi da tarzoma, tare da ƙwato bindigogi 31.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rabi Laxmi Chitrakar zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce
Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar Tanzania ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasar mai cike da ruɗani.
Hukumomin zaɓen ƙasar sun sanar da cewa Shugaba Samia Suluhu ta lashe zaɓen ne da kashi 97 na kuri’un da aka jefa.
Hukamar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa mutum 31,913,866 ne suka kaɗa kuri’a a zaɓen, wanda ya gudana a yayin da kasar ke fama da ƙazamar zanga-zanga.