Shugaban Rikon Kwaryar Gwamnatin Siriya Ya Ce: Sabanin Siriya Da Iran Ba Na Dindindin Ba Ne
Published: 13th, September 2025 GMT
Shugaban rikon kwaryar Siriya ya bayyana cewa; Babu sabani na dindindin da Iran
Shugaban rikon kwarya na Siriya Abu Mohammed al-Jolani ya yi magana kan alakar Siriya da sauran kasashe, inda ya mai da hankali kan Rasha, Iran da Masar. Ya kuma yi jawabi game da zaben Siriya da ayyana kundin tsarin mulkin kasar da kuma abubuwan da suka faru a lardin Suweida na kasar.
Shugaban rikon kwaryar ya fada a jiya Juma’a cewa: Kasarsa ta yi saurin sake gina huldar dake tsakaninta da kasa da kasa, kana ta samu goyon baya daga galibin kasashe musamman na yankin. Ya yi nuni da cewa, ba za a so a kasance cikin halin damuwa da wata kasa ba, kuma kwallon tana cikin kotunan kasashen da ke son tada fitina.
Dangane da alakar da ke tsakaninta da Rasha, al-Jolani ya ce, kasa ce mai muhimmanci, mamba a kwamitin sulhu, kuma akwai alaka ta kut-da-kut da ita, wanda dole ne a kiyaye. Ya kara da cewa, a lokacin da ya kira yakin ‘yantar da kasar, an yi shawarwari da Moscow, kuma Rashan sun nisanta kansu daga yakin tare da ficewa daga fagen soji bisa yarjejeniya.
Dangane da Iran, al-Julani ya yi la’akari da cewa “akwai sabani mai zurfi, amma hakan baya nufin sabani na dindindin ba ne, da zai hana kyautata alaka tsakanin kasashen biyu.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jami’in Kungiyar Hamas Ya Yi Tsokaci Kan Yunkurin Kashe Tawagar Kungiyar Ta Hamas A Doha September 13, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Ko Suka Jikkata Sun Karu September 13, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Muhimman Wurare A Haramtacciyar Kasar Isra’ila September 13, 2025 MDD ta goyon bayan kafa kasar Falasdinu da gagarimin rinjaye September 13, 2025 Pezeshkian zai halarci taron Doha kan Isra’ila September 13, 2025 Turkiyya ta yi tir da harin da Isra’ila ta kai Qatar September 13, 2025 Sharhin Bayan Labarai: Qatar Zata Sauya Amurka A Matsayin Abokiyar Tsaron September 13, 2025 Gaza : Adadin shahidai A kisan kare dangi na Isra’ila ya kai 64,756 September 13, 2025 Unicef : Yara na cikin ukuba sanadin shingen Isra’ila a Gaza September 13, 2025 Araqchi: Babu Dalilin Jin Tsoron Tattaunawa September 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadi a matsayin martani ga sanarwar Washington na ci gaba da gwajin makaman nukiliya, yana mai kiran hakan a matsayin wani mataki na koma-baya da Rashin yin da’a ga dokokin kasa da kasa.
Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya soki Washington saboda sauya wa Ma’aikatar Tsaron kasar suna zuwa Ma’aikatar Yaki, kuma ya yi Allah Wadai da Shirin Amurka na yin gwajin makaman nukiliya, tare da bayyana hakan a matsayin yunkurin tayar da zaune tsaye da jefa duniya a cikin bala’i.
Wanda yake aikata irin wannan halayya ne ke ci gaba da yin barazanar sake kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Iran bisa hujjar hana Iran mallakar makaman nukiliya da sunan kare kansu daga Iran domin kada ta mallaki makaman kare dangi.” in ji ministan harkokin wajen Iran.
Ya yi Allah wadai da Amurka saboda sukar da ta dade tana yi wa shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran yayin da ita kuma take ci gaba da gwajin makamanta na nukiliya, wanda hakan ya saba wa dokokin duniya.
Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Laraba ya bayyana cewa makaman nukiliya na Washington su ne mafi girma a duniya, kuma ya danganta wannan matsayin da gyare-gyare da aka yi a lokacin gwamnatinsa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci