Tsohon Kwamandan IRGC Ya Ce Boma-Boman HKI Na Zuwa Kanku Idan Kunki Samar da Kawance
Published: 14th, September 2025 GMT
Tsohon kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Mosen Razai ya bayyana cewa kasashen yanking abas ta tsakiya su saurari fadowar boma boman HKI a kan kasashensu idan sun ki daukar matakin hada kai da kuma samar da rundunar kawance don fuskantar haramtacciyar kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rezayi yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa, kasashen Saudiya, Turky da Iraki su jira randa boma-baman HKI zasu fada a kan kasashensu.
Rezai ya bayyana haka ne rana guda kafin a fara taron gaggawa na kasashen larabawa da musulmi a yau lahadi a birnin Doha na kasar Qatar.
Ya ce idan taron na Doha ya kasa samar da kawaice kasashen don fuskantar yahudawan , har aka waste, to kasashen Saudia da Iraki da turkiyya sun jira randa jiragen yakin HKI zasu yi luguden wata a kan kasashensu.
Rezai wanda ya kasance mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa ya zuwa yanzu HKI ta kai hare-hare ko kuma tana mamaye da wasu kasashen yankin wadanda suka hada da Lebanon, Yemen, Siriya , Qatar da kuma Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka HKI Tana Ci Gaba Da Rusa Dogayen Gine-Gine A Gaza A September 14, 2025 Dubban Mutanen New Zealanda Sun Fito Jerin Gwanon Goyon Bayan Falasdinawa September 14, 2025 Velayati: Taron Malaman Yahudu A Azerbaijan Tsokana Ce Ga Musulmi Shia September 14, 2025 Wajibi Ne Kasashen Musulmi Su Dauki Mataki Wajen Kawo Karshen Rashin Hankalin Isra’ila. September 13, 2025 Sojojin Isra’ila Sun Kashe Masu Neman Agaji 4 Tare Da Jikkata Da Dama A Gaza. September 13, 2025 Kasar Masar Ta Gano Makircin Isra’ila Na Kashe Shuwagabannin Hamas A Kasar Ta September 13, 2025 Alakar Iran Da Tunusiya Ta Nuna Aniyar Iran Ta Alaka Da Kasashen Musulmi. September 13, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Kudurin Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinu September 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce: Akwai Yiwuwar Sake Tattaunawa Da Jami’ar Tarayyar Turai September 13, 2025 Shugaban Rikon Kwaryar Gwamnatin Siriya Ya Ce: Sabanin Siriya Da Iran Ba Na Dindindin Ba Ne September 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da cewa daga lokacin da aka tsayar da wuta zuwa yanzu adadin Falasdinawan da HKI ta kashe sun kai 200, yayin da wasu kusan 600 sun jikkata.
Sanarwar ta ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta kuma ci gaba da cewa; A cikin sa’o’i 48 da su ka gabata,an sami shahidai 22, biyar daga cikinsu basu dade da yin shahada ba, sai kuma 17 da aka tono su daga karkashin baraguzai. Haka nan kuma na kai wasu 9 zuwa asibitocin da suke a yankin.
Wani sashe na sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ya ce, har yanzu da akwai shahdai masu yawa da suke a karkashin baraguzai, wasu kuma a kan hanyoyi, saboda rashin kayan aiki da kungiyoyin agaji za su yi amfani da su.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu, adadin shahidai ya kai 68,858, sai kuma wani adadin da ya kai 170,664 da su ka jikkata.
Amma daga tsayar da wuta a ranar 11 ga watan Oktoba zuwa yanzu, an sami shahidai da sun kai 226, sai kuma wasu 594 da su ka jikkata. Haka nan kuma an iya tsamo gawawwakin shahidai daga cikin baraguzai har su 499.
Haka nan kuma ma’aikatar kiwon lafiyar tra sanar da karbar gawawwaki 30 da HKI ta mika wa bangaren Falasdinawa ta hannun hukumar agaji ta “Red-Corss.
Tun bayan tsagaita wutar yaki, har ya zuwa yanzu dai HKI tana ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci