Amfani Da Karfin Tuwo Ba Zai Iya Kawo Zaman Lafiya A Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba
Published: 11th, September 2025 GMT
A yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta soki lamirin harin da aka kaddamar a birnin Doha, fadar mulkin kasar Qatar a jiya Talata, tana kuma adawa da matakin Isra’ila na cin zarafin ikon mulkin kasa da tsaron kasa na Qatar.
Lin Jian ya ce kasar Sin na kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, musamman Isra’ila, da su kara kokari wajen dakile rikicin, da sake fara tattaunawa maimakon akasin hakan.
Dangane da sanarwar da Isra’ila ta gabatar wa Amurka kafin ta kaddamar da harin ta sama, Lin Jian ya bayyana cewa, matakin da Isra’ila ta dauka na da alaka da rashin daidaito da wasu kasashen suke nunawa a tsawon lokaci kan batun Gabas ta Tsakiya.
Ya ce ana kira ga wasu manyan kasashen duniya da su ba da gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da tabbatar da adalci, da sauke nauyin dake wuyansu, da hada kai da kasashen duniya wajen taka rawa mai ma’ana ta inganta tsagaita bude wuta da saukaka rikicin yankin. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Isra’ila ba za ta kai hari kan Iran ba sai da goyon bayan Amurka
Ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ba za ta kaddamar da yaki kan Jamhuriyar Musulunci ba tare da samun wata kariya daga Amurka ba. Ya kara da cewa, Iran ta gudanar da yakin kwanaki goma sha biyu da wannan gwamnati mai wuce gona da iri, kuma ta hana ta ci gaba da mummunar manufarta ta mamaya a yankin.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Al- Jazeera, Araqchi ya yi nuni da cewa: Gwamnatin masu wuce gona da iri ta yi kokarin fadada yakin zuwa yankin ta hanyar kai hari kan cibiyoyin man fetur na Iran, amma Iran ta yi nasarar shawo kan yakin kuma ta hana aukuwan hakan.”
Yayin da yake fayyace shirye-shiryen Jamhuriyar Musulunci ta Iran na tattaunawa don kawar da damuwar da ake da ita game da shirin makamashin nukiliyarta na zaman lafiya, Ministan Harkokin Wajen ya jaddada cewa: “Sun shirya wa duk wani abu da zai faru kuma suna tsammanin duk wani hali mai tsauri daga ‘yan sahayoniyya.” Ya bayyana cewa Iran ta samu kwarewa mai yawa daga yakin da ta yi kwanan nan kuma ta samu damar gwada makamai masu linzaminta a wannan yaƙi na gaske.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Larijani: Iran Ba Ta Tsoron Gudanar Da Tattaunawa, Amma Ta Zama Mai Amfani November 2, 2025 Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza November 2, 2025 Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher November 2, 2025 IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci