Ayatullahi Khatami Ya Gargadi Kasashen Larabawa Kan Hare-Haren Gwamnatin Mamayar Isra’ila
Published: 12th, September 2025 GMT
Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran ya gargadi kasashen Larabawa game da harin da gwamnatin mamayart Isra’ila ke kaiwa kan kasashe
Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya gargadi gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila za ta kai musu hari idan har ta samu iko, yana mai jaddada cewa, hanyar tunkarar haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya ita ce mayar da martani mai karfi kanta.
Limamin Sallar Juma’ar na Tehran ya bayyana a cikin hudubarsa cewa: “A matsayinsa limamin sallar Juma’ar Tehran, yana cewa, kuma dole ne gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya su ji cewa: Idan haramtacciyar kasar Isra’ila ta iko, za ta kai hari gare su, taken Netanyahu shi ne ‘Kafa Babban Isra’ila’ ma’ana daga kogin Nilu zuwa Kogin Yufiretis, kuma yana son kwace wasu sassan kasashe a Masar da Jordan.
Limamin Sallar Juma’ar na birnin Tehran ya kuma yi tsokaci kan harin baya-bayan nan da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan kasar Qatar da hedkwatar kungiyar Hamas, yana mai cewa: Halin wannan yahudawan sahayoniyyar shi ne zubar da jinin bil’adama, kuma an kirkire ta ne shekaru 80 da suka gabata da nufin zubar da jini. Ya kara da cewa: “Kada ku yi shakkun cewa tabbas Amurka na da hannu a wannan aika-aika, sararin samaniyar kasar Qatar yana karkashin sansanin Al-Udeid na Amurka, to ta yaya ba za su sani ba?” Wasu kuma sun ce ya zama wajibi Isra’ila ta aiwatar da wannan farmaki, kuma Trump ya ce ya yi bakin ciki ba don ta kai wa Qatar hari ba, sai don ta gaza, kuma shugabannin Hamas sun tsira.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kisan Kiyashin Kan Falasdinawa Da Sojojin Mamayar Isra’ila Ke Yi A Yau Ya Lashe Rayukan Mutane 48 September 12, 2025 Tafiya Sallah Ta Kubutar Da Shugabannin Kungiyar Hamas Daga Kisan Gillar Gwamnatin Mamayar Isra’ila September 12, 2025 Qatar : shugabannin Isra’ila na kishirwar jefa duniya cikin rikici September 12, 2025 Guteress ya tattauna da Araghchi kan shirin shurin nukiliyar Iran September 12, 2025 Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa September 12, 2025 Araghchi ya caccaki kasashen Turai kan yin biris da cin zarafin Amurka da Isra’ila kan Iran September 12, 2025 Venezuela ta yi gargadi game da karuwar sojojin Amurka a cikin tekun Caribbean September 12, 2025 Kwamitin Sulhu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai kan Qatar September 12, 2025 Al-Houthi: Sakamakon samun goyon baya Isra’ila tana ci gaba da aikata laifuka a yankin September 12, 2025 Kasashen Iran da Tunisiya sun amince da fadada alaka yayin da FM Araghchi ya ziyarci kasar Tunisiya September 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Sallar Juma a Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya fada wa Shugaban Amurka Donald Trump cewa; a Nigeria ba a lamunta da duk wani rikicin addini.
Shugaban na kasar Najeriya ta mayar wa da Tinubu martani ne saboda yadda ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai jawo damuwa ta musamman”, bisa zargin cewa Mabiya addinin kiristanci suna fuskantar barazanar karewa, ya kuma yi alkawalin cewa Amurkan za ta ba su kariya.
Donald Trump ya ce; Kiristoci suna fuskantar barazanar karar da su a Nigeria, an kuma kashe dubban kiristoci a kasar.”
A yau Asabar, kwana daya daga wancan zancen na Tinibu ne dai shugaban kasar ta Nigeria Bola Ahamd Tinubu mayar da martanin da ya kunshi cewa: Nageria kasa ce ta Demokradiyya, kuma tsarin mulkinta ya lamuncewa kowa ‘yancin yin addini.”
Har ila yau shugaban kasar ta Najeriya ya ce; Tun daga 2023 gwamnatinmu take mu’amala da hulda da dukkanin malaman kirista da musulmi, kuma tana ci gaba da magance matsalar tsaro da ta shafi dukkanin mutanen kasar daga kowane addini a cikin yankunan kasar.
Shugaba Tinubu ya kuma ce; Bayyana Nigeria a matsayin kasa wacce ake fada da addini, ba ya nuni da hakikanin yadda rayuwa take a kasar, kuma ba a yi la’akari da yadda gwamnati take aiki tukuru domin kare ‘yancin yin addini da akidun mutanen Nigeria ba.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci