Leadership News Hausa:
2025-09-17@20:32:14 GMT

Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara

Published: 15th, September 2025 GMT

Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara

A ƙalla fasinjoji 17 ne suka rasa rayukansu bayan wata motar haya ta faɗa cikin wata gada da ta ruguje a kan titin Gwalli da ke ƙaramar hukumar Gummi, jihar Zamfara.

A cewar hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zamfara, hatsarin ya faru ne a daren Lahadi lokacin da motar ɗauke da kaya da fasinjoji ta faɗa cikin gadar da ta ruguje.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SRC Isah Aliyu, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Kwamandan FRSC na jihar, CC Aliyu Magaji, wanda ya ziyarci wurin hatsarin, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa da asarar rayukan, inda mafi yawansu mata ne. Ya ce hatsarin ya biyo bayan nauyin da aka ɗora wa motar fiye da ƙima da kuma tafiya da daddare.

Hukumar ta gode wa mazauna yankin da suka gaggauta taimakawa wajen ceto wasu daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su. Kwamanda Aliyu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Zamfara da al’ummar Gummi, tare da yin kira ga direbobi su rika bin ƙa’idojin hanya da kuma guje wa tuƙa mota da dare domin kare rayuka.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Hatsari Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa

Nijeriya dai ta daɗe tana fama da ta’addancin Boko Haram da ISWAP a Arewa Maso Gabas.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
  • Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo
  • ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Hakimi Yankan Rago A Zamfara
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara