Kwankwaso Ya Gana Da Shugabannin NNPP A Kuros Ribas Don Tunkarar Zaɓen 2027
Published: 10th, September 2025 GMT
Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma dan takararta na shugaban kasa a 2023, Rabiu Kwankwaso, a ranar Talata ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Kuros Ribas domin tsara dabarun tunkarar babban zabe na 2027.
Da yake jawabi a babban birnin jihar, Kalaba, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su ba da fifiko kan hadin kai da karfafa jam’iyyar a fadin jihar.
Ya ce, “Ina godiya ga daukacin shugabanni da ‘yan jam’iyyar NNPP na Jihar Kuros Riba, ina so in yi amfani da wannan dama domin in gode muku da kuka karɓe mu, muna matukar farin ciki da shugabancin jam’iyyar a jihar, ina kara baku kwarin guiwa da ku yi aiki tukuru don ganin an samu hadin kai a cikin jam’iyyar”.
Ya kara da cewa, dole ne jam’iyyar ta yi aiki da “zuciya daya” idan har tana fatan lashe zaɓukan jihohi da na kasa a 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Zurfafa Dunkulewar Kasuwannin Kasa Ta Bai Daya”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp