Yadda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Suka Yi Maulidin Cikar Annabi (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa
Published: 12th, September 2025 GMT
Wanna taro yana da matukar muhimmanci, taro ne na murnar Annabi SAW, taro ne da haka Halitta ta saba. Duk al’umma tana farin ciki da murnar haihuwar wani mai girma acikinsu, ko wani wanda ya kawo musu cigaba ta hanyar rayuwa ko cigaba ta hanyar kasarsu ko kowa ma yana murnar ranar haihuwarsa, kamar yadda Annabawa suka yi murnar ranar haihuwarsu.
Wannan shi ne abinda ya tara mu a wannan rana ta Maulidin cikar Annabi SAW shekara 1,500 da haihuwa, wannan murna ce kan murna.
Duk wanda yake shekara 30 da haihuwa a yanzu (2025), ya ga lokacin da duniya ta yi bikin cikar Annabi isa AS shekara 2,000 da haihuwa a shekarar 2000, Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da manyan kasashen duniya sun yi murnar wannan rana har da kasashen Musulmi saboda Annabi Isah na kowa ne, to me zai hana Musulmin duniya murnar bikin cikar Annabi SAW shekara 1,500 da haihuwa ba? Kuma Allah ya sa mun ga wannan rana, tun da mun zo a wannan zamani, kuma ba za muga shekarar da Annabi SAW zai cika 2,000 da haihuwa ba sai dai jikokin jikoki, mu kuma mun zama mutanen da, sai kaji suna cewa, kakanninmu sun ga zamanin da Annabi SAW ya cika shekara 1,500 da haihuwa. Da wannan muke cewa, za a kai lokacin da jikoki za su yi murna kakannin su sun ga wannan rana ta 1,500 kuma sun yi murna da ita. Kamar yadda na baya suka yi murna da cikar Annabi 1,000 har zuwa 500 (karewar Daular Abbasawa) har zuwa kan sahabbai da suka yi zamani da Annabi SAW.
Dangane da sabanin fahimta da ke dabaibaye da batun Maulidin Annabi SAW, Shehu Almadda ya yi karin haske da cewa, kowane dan Adam yana nan rike da tarihin kakanninsa da iyayensa, don haka, yana daga cikin sakaci da aka tusawa samari a wannan zamani, rashin girmama tarihin Annabinsu. Abin takaici, kaga mutum yana kiyaye tarihin shugabansa na siyasa, makaranta, wurin sana’a amma Annabinsa ko oho!!! Kowace al’umma tana alfahari da Annabinta, amma sai mu Al’ummar Annabi ne kadai za mu ce ba haka ba. Girmama Annabi shi ne girmama Addininsa, girmama addinninsa shi ne girmama kanmu. Rashin girmama Annabi shi ya jawo rashin girmama addini, shi ya jawo rashin girmama kanmu, kuma shi ya jawo duk abinda ke faruwa yanzu ke faruwa.
Annabi Muhammad SAW, mahaifinsa Abdullahi da mahaifiyarsa Aminatu, an haife shi a Makkah, sai da ya cika shekara 40, sannan Allah ya aiko shi don ya isar da sakonsa tabaraka wata’ala. Shi yafi kowa sanin Allah, shi ya gaya mana akwai Allah, mu kadai ta shi, Allah ya hado shi da Alkur’ani wanda ya tattaro mana duk hukunce-hukuncesa aciki. Annabi SAW ya yi zaman Annabta har na tsawon shekara 13 a Makkah sannan ya yi Hijira zuwa Madina ya yi shekaru 10 sannan ya koma ga Ubangiji. Bayan rasuwar Annabi SAW, sahabbai sun fara kirgar Kalenda da Hijira, yau Hijira 1447, in muka hada ta da shekarun Annabi SAW (40 + 13 + 10 + 1447 = 1,500).
Alkur’ani kuma zai cika shekara 1,500 da saukarwa nan da shekaru 40 masu zuwa. Wannan ba karamin alkairi ba ne, don haka muke Azumin watan Ramadan. Kowane littafi, yana samun girma ne da girman wanda aka saukar mawa, don haka, Littafin da aka saukarwa Annabi Muhammad SAW, ya fi dukkan Littattafan da aka saukarwa Annabawa. Kuma littafin ya yi daidai da kowane zamani, don haka, ake kiran Malamai masu fassara Alkur’ani da su rika fassara shi da irin fahimtar zamaninsu, wayewar zamani da irin ilimin zamani (kimiyya da fasaha).
Duk ilimi, yana karkashin kayayyakin da ake yin sanin da shi, misali, karfin gani na Ido, ba zai yi daidai da yadda dattijo yake gani ba da yadda saurayi ke gani, har ya zama dattijo ya daina gani amma Alhamdulillah, a wannan, zamani sai kwararrun malamai suka kirkiro medikal glass, wanda dattijo zai iya amfani da shi, karfin ganinsa ya zama kamar wani dan saurayi. Da yawan Malamai an yi fatawar a daina amfani da karatunsu a lokacin da suka tsufa sabida ba sa iya ganin littafinsu, da akwai glass na ido a wancan lokaci da ba a yi musu wannan fatawa ba. Bayan Medikal glass na gani akwai wanda yafi shi karfi na binciken kwayoyin halitta (microscope), sannan akwai kuma na hangen sararin samaniya da NATA ke amfani da shi (Telescope). Ma’ana kowane kayan Ilimi akwai inda ya dace da shi.
Malamai suna fassara ‘Jifanin kal jawabi, wa kudurir rasiyat’ da cewa manyan farantai na cin abincin rundunar yaki, amma a wannan zamani, Malamai suka ce a’a, (Satelite signal ne da tukwanen Nukiliya) Allah ke nufi, kuma saboda irin wannan fasaha ta Annabi Sulaiman ce ta janyo sarauniya Balkisu ta musulunta a lokacin da ta shiga masarautar shi har ta dimauta saboda ganin fasahohi.
Wani masani, Morris Bukay a wuraren 1960, ya bayyana cewa, Alkur’ani ya fi karfin ilimin Larabawa, ya fi karfin ilimin zamanin da ya sauka da wanda ya zo bayansa, kuma ya fi karfin ilimin na turawa na wannan karni na 19 kuma ya fi karfin ilimin zamanin da zai zo nan gaba. Saboda wannan yabo, Sarki Faisal ya yi masa kyauta. Morris Bukay, shi ya yi littafin fassarar Alkur’ani inda ya kwatanta Ilimin Alkur’ani da fasaha da Injila (Bible) acikin littafinsa mai suna “The Bible, the kur’an, and Science”.
Har ila yau, dangane da makasudin taron, Almadda ya yi karin haske da cewa, batun Maulidi Haram ne ko ya inganta ko bai inganta ba, DAkIkANCI ne, an wuce wannan zamani, a yanzu batun tarihi ake yi na tina ‘yan mazan jiya a zamanance, a duniyance, a ilimance haka kuma a lahirance. Duk 1 ga Oktoba, Nijeriya tana murnar ranar ‘yancin kai, muna taya wadanda suka samo mana ‘yancin kai don mu rike kasarmu da kyau. Haka kowane gwarzon namiji, in ranar haihuwarsa ta zagayo, yakan tara ‘yan uwa da abokan arziki da yaransa don tayasa murna. Haka yake a kowace kasa, hatta Saudiyya tana murnar ranar ‘yancin kai da suke jira “janadariyya”, sarakunanta da ganguna rike da takubbuna domin ranar ‘yancin kai amma ai yafi da cewa, su yi murnar ranar da Annabi SAW ya ‘yantar da Makkah daga Gumakan da ke cikin Ka’aba.
Don haka, kowa ya rike wannan, a tarihi BA HARAM ko HALAL sai dai GASKIYA ko kARYA, misali, Annabi Muhammad SAW an yi shi har ya zauna a Makkah da Madina ga hujjoji ko kuma wani ya ce, karya ne, mun je mun yi bincike babu wannan lamari. To mu fahimci wannan taro, tarihin Annabi SAW, Allah ya yi mana tarihin Annabawa da yawa a Alkur’ani, ya yi mana tarihin dan Adam, ya dace al’umma ta waye, batun tarihi babu batun Bid’a ko haram sai dai GASKIYA ne tarihin ko kuma akasin haka.
Daga karshe, Mai Diwani ya yi kira ga sauran Malamai shugabannin al’umma da cewa, su yi koyi da zaman Annabi SAW a Madina (Birni), me yasa ya sanya mata Birni bai ce garin Musulmai ba? Saboda birni, shi ne mai sauyawa, bai tsayawa akan abinda ake cewa, “na mu ne, ko kuma haka muka gada” (kauye). Allah ya yi alkawarin halakar da kauye, ma’ana, wanda bai sauyawa, wata rana sai an nemi abin an rasa. Don haka, Annabi SAW ya fita daga Ummul kura (Makkah) saboda babu yadda za a yi a canzata, dakin kakanni ne, ba zaka zo da sabo ba wanda ba nasu ba, ya tafi Madina inda ya kafa kundin tsarin mulki na farko mai suna “wasikatu Madina”, duk wanda yake Madina, dan kasa ne a zauna tare a kiyaye kasa tare kuma a gudu tare, ya yarda Yahudawa, Nasara, Munafikai da wadanda ba za su bi shi ba duk a zauna wuri daya a zauna lafiya, duk abunda ya faru, warware tsarin kundin mulki ne ya jawo Annabi SAW ya hukunta su.
Annabi SAW ya fada cewa, duk in addininsa ya cika shekara 100, Allah zai kawo wani ya sabunta shi saboda ya tsufa, fahimtarsa ta tsufa, a nan zamu fahimci cewa, in har duk bayan shekara 100 Allah zai tura wani ya sabunta addini, yau Addininmu yana kan shekara 1447, don haka, ya zama dole Malamai su waye.
Sannan ya yi kira ga ‘yan kasa, su amsa kiran hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) wurin yin katin zabe domin kowa ya zabi ra’ayinsa kuma ‘yancinsa ne domin shi dan kasa ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027.
Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta.
Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo“Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa. Wannan yana nuna cewa ba sa son a samu hamayya a lokacin zaɓe,” in ji shi.
Galadima ya kuma yi gargadi kan shirin nada wani da ya kira mai lam’a a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), yana mai cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin rudani.
“Ina fatan ba gaskiya ba ne, domin idan wannan mutumin ya zama shugaban INEC, ka tabbata cewa wannan gwamnati na neman tayar da yaƙin basasa,” in ji shi.
Sai dai bai ambaci sunan mutumin ba.
Dangane da batun fara yaƙin neman zaɓe da wuri da wasu jam’iyyu ke yi, Buba Galadima ya zargi INEC da gazawa wajen aiwatar da tanade-tanaden dokokin zaɓe.
“Wannan batun fara yaƙin neman zaɓe kafin INEC ta ba da izini, gwamnatin da ke kan mulki ce ta fara shi. Wannan yana nuna cewa INEC ba za ta iya zama mai adalci a irin wannan yanayin siyasa da muke ciki ba,” in ji shi.