Iran Ta Zama Zakara A Wasan Kwallon Kafa Ta Bakin Teku Karo Na 4 Asiya
Published: 31st, March 2025 GMT
Yan wasan kwallon kafa na kasar Iran sun zama zakara karo na 4 a kwallon kafa na yashin bakin teku a karo na 4 a cikin kasashen Asiya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ba bayyana a gasa ta karshe wanda kungiyar kwallon kafa ta yashin bakin take wanda aka gudanar tsakanin JMI da kuma Omman an tashi da ci 8-1.
Wannan nasarar dai ta tabbatar wa kasar Iran fifiko a wannan wasar har saw hudu a jere. Kuma ba’a taba samun nasara a kan ta gaba daya a dukkan wasannin da ta yi a duk tsawon gasar ba.
Mai horar da yan wasan Iran a wannan gasar Ali Nadiri ya bayyanawa IP kan cewa nasarar da JMI ta samu a wanna gabasa ya tabbatar da kokarinsu a wanna wasar, sannan da hadin kansu a wannan wasar wanda kuma hakan yake basu nasara a duk wasan da suka yi. Don haka muna alfakhari da sake maida wannan kofin gida Iran inji Nadiri.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya
Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya ta naɗa Sheikh Bashir Aliyu Umar a matsayin shugabanta bayan rasuwar Sheikh AbdulRasheed Hadiyyatullah.
Wata sanarwa da majalisar ta fitar a yau Laraba ta ce an amince da shuagabancin Dokta Bashir ne kai-tsaye saboda kasancewarsa mataimakin shugaba.
A ranar Litinin ne Sheikh Hadiyyatullah ya rasu yana da shekara 81 a Jihar Osun.
“Nan gaba za a sanar da mataimakin shugaban,” in ji sanarwar da Nafiu Baba Ahmed ya sanya wa hannu a matsayin sakataren majalisar.
Sheikh Bashir sanannen malami ne kuma shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke Alu Avenue a Unguwar Nasarawa ta Jihar Kano.