Jakadan Kasar Rasha A Saliyu Ya Ce Kasar Rasha Tana Nazarin Yiyuwar Fara Hakar Ma’adinin bauxite A Kasar
Published: 30th, March 2025 GMT
Kamfanin hakar ma’adinai mai suna RUSAL na kasar Rasha ya aika da tawaga zuwa kasar Saloyo a yammacin Afirka don nazarin yiyuwar fara hakar ma’adinin bauxite a kasar nan gaba.
Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya nakalto jakadan kasar Rasah a Saliyo yana fadar haka.
Labarin ya nakalto Mohammad Yongawo wani jami’in gwamnatin kasar ta Saliyo yana cewa kasarsa a shirye take ta kammala yarjeniya tsakanin kamfanin Rusal na kasar Rasha don fara aiki a yankunan da ske da ma’adinin bauxite.
Kafin haka dai ministan ma’adinai na kasar ta Saliyu Julius Mattai ya fadawa kamfanin dillancin labaran Sputnik kan cewa an fara tattaunawa tsakanin gwamnatinsa da kamfanin a birnin Free Town.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Rasha
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine
Fadar Kremlin ta kasar Rasha ta ayyana tsagaita wuta na kwana biyu ita kaɗai a yakinta da kasar Ukraine.
Shugaba Vladimir Putin ya sanar a ranar Litinin cewa Rasha za ta aiwatar da tsagaita wutar ne daga tsakar dare na 8 ga Mayu zuwa tsakar dare na 10 ga Mayu.
A ranakun da za a tsagaita wutar ne Rasha ke bikin karshen da yakinta da kasar Jamus a shekarun 1941 zuwa 1945, wanda aka fi sani da Yakin Duniya na Biyu a yawancin duniya.
A Rasha ana kiran yakin na Duniya na biyu da sunan Babban Yaƙin Ceton Kasa.
Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji laifi ne — Janar Chibuisi