Gaza: Fararen hula 22 sun yi shahada a hare-haren Isra’ila a daren jiya
Published: 7th, August 2025 GMT
Hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza a daren jiya ya yi sanadiyar shahadar Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu masu tarin yawa, yayin da jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kaddadamar da munanan hare-hare a kan a yankuna da dama na Zirin da aka yi wa kawanya, da suka hada da gidajen farar hula da tantunan da aka kafa a mafaka ga iyalan da suka rasa matsugunansu.
A cewar wakilin Al Mayadeen, akalla Falasdinawa biyar ne suka yi shahada, wasu kuma suka jikkata bayan da jiragen saman Isra’ila suka yi ruwan bama-bamai a wani tanti da ke a yankin Tal, kudu maso yammacin Deir al-Balah a tsakiyar Gaza.
A sansanin Nuseirat na yammacin Gaza, wani jirgin sama mai saukar ungulu na Isra’ila ya kai hari kan wani gida da ke hasumiyar al-Salhi kusa da unguwar Abu Serrar, inda ya kashe Anas Abdul Rahman al-Jammal, da matarsa, da ‘ya’yansu mata biyu. Harin ya kuma yi sanadiyyar jikkata wasu fararen hula.
An samu karin hasarar rayuka bayan harin da Isra’ila ta kai kan iyalan da suka rasa matsugunansu a sansanin ‘yan gudun hijira na al-Bureij, da ke tsakiyar zirin Gaza.
A kudancin zirin Gaza, hare-haren da jiragen yakin Isra’ila suka kai a yankin al-Mawasi dake yammacin Khan Younis, sun yi sanadin shahadar da dama daga cikin fararen hula da suka hada da wani karamin yaro mai suna Amir Mansour mai shekaru 6 tare da mahaifiyarsa.
Hakazalika jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a sansanin Khan Younis da ke yammacin Gaza, inda suka kashe Ahmad Rubhi Abu Sahloul, da matarsa, da ‘ya’yansu bayan sun kai hari a gidansu da ke unguwar al-Qatatwa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Pezeshkian Ya Jaddada Wajabcin Haduwar Kasashen Musulmi Wajen Hana Laifukan Yaki A Gaza August 6, 2025 Araqchi Ya Taya Larijani Murnar Zama Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran August 6, 2025 Japan: An Fara Juyayin Cikar Shekaru 80 Da Harin Amurka Na Makamin Nukiliya A Hiroshima August 6, 2025 Sudan: Dakarun RSF Sun Kashe Fararen Hula 14 Tare Da Jikkata Wasu Na Daban August 6, 2025 IRGC: Bayan yakin Kwanaki 12 Yanayi Ya Sauya Zuwa Ga Amfani Ga Iran August 6, 2025 ‘Yansanda A Iran Suna Amfani Da Kayakin Tsaro Na Zamani A Lokacin 40 August 6, 2025 Iran tana Goyon Bayan Zaman Lafiya Tsakanun Kasashen Yankin August 6, 2025 Azizi: Iran Ba Za Ta Bar Wani Ya Kusanci Cibiyoyinta Na Tace Sanadarin Uranium Ba August 6, 2025 Iran: Yakin Kwanaki 12 Ya Bayyana Inganci Da Karfin Yakin Yanar Gizo Na Kasar August 6, 2025 Iran: An nada Larijani a matsayin sakataren kwamitin koli na tsaron kasa August 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Mutanen Gaza Kisan Kiyashi
A daidai lokacin da aka shiga cikin kwanaki na 718 da fara yakin Gaza, HKI tana ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi da makamai da kuma yunwa.
Majiyar Falasdinawa ta tabbatar da cewa daga safiyar yau Talata zuwa tsakiyar ranaFalasdinawa masu yawa sun yi shahada.
Majiyar dai ta ce, jiragen yakin ‘yan sahayoniyar sun kai hare-hare akan wani gida da yake a gabar ruwa a yammacin Gaza. Haka nan kuma da safiyar yau Talata din sojojin HKI sun kai hari da manyan bindigogi a yankin arewacin birnin Gaza.
Wasu yankunan da HKI ta kai wa hare-haren sun hada titin Umar Mukhtar a tsohon garin birin Gaza.
A unguwar Tal-hawa ma sojojin mamayar sun kai wasu hare-hare akan gidajen fararen hula a yammacin birnin Gaza. Sai kuma wasu makarantun da suke a karkashin Unruwa da kan titin “al-Nasr” dake yammacin birnin Gaza.
Daga fara yakin Gaza a 2023 zuwa yanzu adadin wadanda su ka rasa rayukansu sun kai 65,344, sai kuma wadanda su ka jikkata da sun kai 166,795. Haka nan kuma da akwai wasu Falasdinawan da sun kai 9,000 da ba a san inda su ka shiga ba.
Kisan kiyashin da HKI take yi wa Falasdinawan dai yana faruwa ne a karkashin cikakken goyon bayan Amurka, da kuma shiru da rufe idanu na sauran kasashen turai da abinda ake kira kungiyoyin kasa da kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Nato Na Yin Taron Tattaunawa Keta Hurumin Samaniyar Kasar Estonia Da Rasha Ta Yi September 23, 2025 Dembele Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Shekara Ta 2025. September 23, 2025 Hindi: Amurka Da Kasashen Yamma Ba Sa Son A Dakatar Da Bude Wuta A Gaza. September 23, 2025 Tattalin Arzikin Najeriya Ya HaBaka A Rubu’i Na Biyu Na 2025 September 23, 2025 Kashi 80 Cikin Dari Na MDD Sun Amince Da Falasdinu A Matsayin Kasa. September 23, 2025 Iran Da Rasha Zasu Rattaba Hannun Kan Batun Gina Wasu Tashoshin Nukiliya. September 23, 2025 Hamas ta bukaci kasashen duniya da MDD su mayar da Isra’ila saniyar ware September 22, 2025 Iran : Dakatar da kisan kiyashi a Gaza, ‘’zakaran gwajin dafi ‘’ne ga MDD” September 22, 2025 Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza September 22, 2025 Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci