Kotun Ta Umurci Gwamnatin Neja Ta Janye Hukuncin Da Ta Dauka Akan Gidan Rediyon Badeggi
Published: 6th, August 2025 GMT
Babbar Kotun Shari’a ta Minna a Jihar Neja ta bayar da wani umarnin na wucin gadi game da gidan rediyon Badeggi Radio Broadcasting Services Ltd, inda ta hana Gwamnatin Jihar ɗaukar duk wata matsaya da za ta dakatar da ayyukan gidan rediyon.
Mai Shari’a Mohammed Mohammed ne ya yanke hukuncin bisa ƙorafin gaggawa (motion ex-parte) da Badeggi Radio Broadcasting Services Ltd da Daraktan gudanarwarta, Mohammed Shuaibu Badeggi, suka gabatar a kotun da ke Minna.
A cikin ƙorafin, lauyoyin masu ƙara sun jingina hujjoji da sassa daban-daban na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara), da kuma Dokar Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC Act).
Hukuncin kotun ya hana wadanda ake ƙara, ciki har da Gwamnan Jihar Neja, Antoni Janar da Kwamishinan Shari’a, da Hukumar Raya Birane ta Jihar Neja, daukar duk wani mataki da zai kawo cikas ga lasisin watsa shirye-shirye ko ayyukan kasuwancin kamfanin dake cikin harabar gidan talabijin na N.T.A a Uphill, Minna.
A yayin yanke hukuncin, Mai Shari’a Mohammed Mohammed ya ce yana da matuƙar muhimmanci a bar komai yadda yake (status quo) har sai an kammala sauraron babbar ƙarar gaba ɗaya.
Umarnin na wucin gadi ya haramta ayyuka kamar soke lasisi, janye lasisi, kwacewa, ko kai farmaki da rushe wurin da kamfanin ke gudanar da ayyukansa.
Lauyan masu ƙara, Barista Philip Emmanuel, ya bayyana jin daɗinsa da hukuncin kotun, yana mai cewa hakan babbar nasara ce wajen kare haƙƙin abokan aikinsa.
An shirya cigaba da sauraron ƙarar a wani lokaci domin zurfafa bincike kan batutuwan da ke gaban kotu.
Daga Aliyu Lawal
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba November 2, 2025
Manyan Labarai 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su November 2, 2025
Manyan Labarai Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya November 2, 2025