Kotu ta hana jagoran adawa Maurice Kamto takarar shugaban ƙasa a Kamaru
Published: 6th, August 2025 GMT
Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban ƙasa, a babban zaɓe mai zuwa na watan Oktoba, kan abin da ta bayyana rashin cika ka’idojin tsayawa takara.
Lauyansa, Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun wanda ba za a iya ƙalubalanta ba, bayan kammala zamanta na wannan Talata.
A cewarsa, kotun ta yi watsi da ƙarar da suka shigar kan matakin hukumar zaɓen ƙasar na cire shi daga cikin jerin ’yan takarar da za su fafata a zaɓen ranar 12 ga watan Oktoban bana.
Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri ’Yan gida ɗaya sun kitsa garkuwar ƙarya domin karɓar N5m a wurin mahaifinsuMista Kamto mai shekaru 71, ya yi ƙaurin suna wajen sukar gwamnatin shugaba Paul Biya, kuma shi ne ya yi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2018, bayan tsayawa takara a jam’iyyar MRC.
A wannan karo kuma ya nemi tsayawa takarar a jam’iyyar MANIDEM, inda ya bayyana muradin tsayawar watanni biyar da suka gabata.
Hukumar zaɓen ƙasar ta yanke hukuncin cire Kamto saboda “’yan takara masu yawa,” bayan wani ɗan takara daga wani tsagin jam’iyyar ya miƙa buƙatar makamanciyar wannan, wanda ya sa ake nuna damuwa kan halascin shugabancin jam’iyyar.
Bayan gabatar da hukuncin, Kamto wanda da alama bai ji daɗin hakan ba, ya fice daga harabar kotun ba tare da magana da ’yan jarida ba.
Hukuncin da aka yanke a ranar Talata ya ƙara tayar da fargabar hargitsi.
An jibge jami’an tsaro a kusa da cibiyar taro da ke babban birnin ƙasar, Yaoundé, inda Kwamitin Kundin Tsarin Mulki ya bayyana hukuncin, da kuma manyan titunan birnin.
A ranar da ta gabata, ’yan sanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye tare da kama mutane da dama da suka fito zanga-zangar goyon bayan Kamto.
Lauyoyinsa waɗanda ba su yi ƙarin bayani kan mataki da za su ɗauka ba, sun ce Kamto ne zai bayyana matakin da zai ɗauka.
Masu suka na ganin cewa akwai wata maƙarƙashiya ne na kawar da ɗan siyasar daga zaɓen.
Duk da raɗe-raɗin rashin lafiya, yanzu haka shugaba Paul Biya mai shekaru 92, wanda ya shafe tsawon shekaru 43 yana mulkin Kamaru, zai sake neman wa’adi na takwas a kan karagar mulki ba tare da wata ƙwaƙƙwarar adawa ba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya Karu
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Duk da karin kudin da gwamnatoci a matakin jiha suke samu daga asusun tarayya, ’yan Najeriya da dama suna korafin ba sa gani a kas.
Manazarta dai sun ce ko kafin karin ma ya kamata ya yi a ce ayyukan da gwamnatcin jihohi suke yi sun fi da ake gani
Ko mene ne ya sa jihohi “ba sa kashe karin kudaden da suke samu yadda ya kamata”?
NAJERIYA A YAU: Yadda Talauci Ke Hana Shayar Da Yara Nonon Uwa Zalla A Najeriya DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aureWannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan