Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Burkina Faso, Mali da Nijar sun fice daga Kotun ICC

Ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da sojoji ke mulki sun sanar cewa sun fice daga Kotun Duniya ta Hukunta Manyan Laifuka (ICC).

A sanarwar da suka fitar ranar Litinin sun bayyana ICC a matsayin “kayan aikin mulkin mallaka na zamani.”

Ƙasashen ukun, waɗanda aka yi juyin mulki a cikinsu tsakanin shekarun 2020 zuwa 2023, sun kafa ƙawance mai suna Kungiyar Kasashen Sahel (AES) domin haɗa kai da nisantar da kansu daga ƙasashen Yamma, musamman tsohuwar mai mulkinsu, Faransa.

A cikin sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, ƙasashen sun ce kotun da ke birnin Hague “kayan aikin danniya ce a hannun masu mulkin mallaka.”

’Yan sanda sun kama mutum 4 kan kai wa Lakurawa babura a Kebbi Faransa ta amince da ’yancin ƙasar Falasɗinu a hukumance

Sun ƙara da cewa, “ICC ta kasa tabbatar da shari’o’in manyan laifuka da suka haɗa da laifukan yaƙi, kisan gilla ga bil’adama, kisan ƙare dangi da kuma laifukan cin zarafin ƙasa.”

Sun ce suna shirin kafa “hanyoyin cikin gida domin tabbatar da zaman lafiya da adalci.”

Doka ta tanadar cewa ficewar kowace ƙasa daga ICC zai fara aiki ne shekara guda bayan an miƙa sanarwar ficewar ga Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya.

Tun bayan kafa AES, Burkina Faso da Mali da Nijar sun ƙara kusanci da ƙasashe irin su Rasha, wadda Shugabanta Vladimir Putin ke fuskantar sammacin kame daga ICC tun watan Maris 2023 kan yaƙin da ake yi a Ukraine.

Sai dai ƙasashen ukun na fama da hare-haren ta’addanci daga ƙungiyoyin masu alaƙa da Al-Qa’ida da Daesh, yayin da ake kuma zargin sojojinsu da aikata laifuka kan fararen hula.

Kotun ICC dai an kafa ta ne a 2002 domin gurfanar da waɗanda suka aikata manyan laifuka — musamman na yaƙi — a inda gwamnati ba ta da ikon ko kuma ba ta da niyyar ɗaukar mataki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Fiye Da Falasdinawa 900,000 Ne Su Ka Yi Hijira A Cikin Gaza
  • Burkina Faso, Mali da Nijar sun fice daga Kotun ICC
  • He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
  • Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS
  • Da Ɗumi-ɗumi: Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 4.32 A 2025
  • Yawan Kudin Da Aka Kashe Na Zamantakewa A Watan Agusta A Kasar Sin Ya Kai RMB Triliyan 3.97
  • Bayan Mutuwar Wani Matashi, An Kafa Dokar Ta Baci A Yauri
  • Birtaniya Ta Amince Da Kafa Falasɗin A Matsayin Ƙasa
  • Iran Da Pakistan Sun Sake Tsara Dangantakarsu Ta Tattalin Arziki
  • Shugaban Kasar Iran Ya Yi Kira Ga Samar Da Tattalin Arziki Da Shugabancin Kwararru