Matar Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Hajiya Hadiza Ahmad Sama’ila Yakawada, ta kaddamar da Makon Shayar da Nono na Duniya na bana, tare da kira ga iyaye mata da mazajensu da su ba wa jarirai nono kacokam na tsawon watanni shida na farko.

A yayin kaddamarwar, Hajiya Hadiza ta bayyana cewa shayar da jarirai nono na da muhimmanci matuƙa wajen tabbatar da lafiyar yara da kuma inganta cigaban su tun daga ƙuruciya.

Ta kuma bayyana cewa makon yana da nufin wayar da kan jama’a musamman a tsakanin iyalai game da amfani da shayar da nono, tare da ƙarfafa gwiwar ma’aikatan lafiya da su ci gaba da fafutukar wayar da kai a fadin karamar hukumar.

A nata jawabin, Sakatariyar Lafiya ta Karamar Hukumar Giwa, Hajiya Salamatu Balarabe, wadda ta sami wakilcin Hajiya Talatu Bello, jami’ar kula da magunguna masu muhimmanci ta karamar hukumar, ta yabawa kokarin shugaban karamar hukumar, Alhaji Ahmad Sama’ila Yakawada, wajen ɗaukar matakai don tabbatar da ingantaccen kula da lafiya ga al’ummar yankin.

Ta ce karamar hukumar za ta ci gaba da himma wajen kyautata lafiyar uwa da yara a fadin Giwa.

COV/Magaji Yakawada 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Giwa LG Kaddamarwa Shayarwa karamar hukumar

এছাড়াও পড়ুন:

Cutar Kwalara ta kashe mutum 58 a Bauchi

Aƙalla mutane 58 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon barkewar cutar Kwalara a ƙananan hukumomi 14 daga cikin 20 da ke jihar Bauchi.

Haka kuma, an samu sabbin mutane 258 da suka kamu da cutar a faɗin jihar.

Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza An yanke wa Soja hukuncin kisa ta hanyar rataya

Mataimakin Gwamnan jihar, Auwal Mohammed Jatau, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da wasu kwamitoci biyu kan yaki da cutar a jihar.

Mataimakin Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda barkewar cutar ke ci gaba da kashe mutane, lalata rayuwar jama’a, da kuma jefa tsarin kiwon lafiya na jihar cikin matsala.

Jatau ya bayyana cewa: “Ana iya kaucewa wannan barkewar cutar idan aka ɗauki matakan gaggawa, aka haɗa kai wajen tunkarar cutar, tare da ci gaba da inganta ruwa, tsafta da kula da muhalli. Jihar Bauchi ta samu sabbin mutane 258 da suka kamu da cutar, tare da mutuwar wasu 58.”

Ya ƙara da cewa duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi, Kwalara na ci gaba da zama barazana ga lafiyar jama’a.

Ya ce kafa kwamitin yaki da cutar ba wai kawai ya zo a kan lokaci ba, har ma yana da matuƙar muhimmanci wajen cimma burin da aka sa gaba na dakile ci gaba da yaduwarta.

A cewarsa: “Wannan kwamitin zai zama ja-gaba wajen jagorancin hukumomin gwamnati a jihar Bauchi kan barkewar Kwalara, tare da tsara dabarun kariya na dogon lokaci da suka yi daidai da Tsarin Ƙasa na Yaki da Cholera da kuma manufofin Cibiyar Dakile Cututtuka ta Najeriya (NCDC).”

Mataimakin gwamnan ya tunatar da mambobin kwamitocin cewa zaɓensu ya nuna ƙwarewarsu, sadaukarwarsu da muhimmancin rawar da za su taka wajen nasarar aikin, tare da fatan za su tabbatar da sa ido, gano cuta da wuri, da kuma ɗaukar matakin gaggawa idan ta barke.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Ɗantsoho Ya Mayar Da Hankali Wajen Farafaɗo Da Martaba Da Ƙimar NPA
  • GORON JUMA’A 19-09-2025
  • Cutar Kwalara ta kashe mutum 58 a Bauchi
  •  Yahudawa Suna Ci Gaba Da Yin Hijira Zuwa Wajen HKI
  • Hukumomin Bada Agajin Gaggawa Sun Bada Horo Kan Aikin Ceto A Karamar Hukumar Auyo
  • Hukumar Bunkasa Ilimin Manyan Makarantu Ta Shirya Taro Na Musamman Ga Jami’anta
  • ‘Yansan Jigawa Sun Tabbatarwa Mafarauta Da ‘Yan Bulala Samun Horo
  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta