’Yan gida ɗaya sun kitsa garkuwar ƙarya domin karɓar N5m a wurin mahaifinsu
Published: 5th, August 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Nijeriya reshen Abuja ta sanar da cafke wasu mata ’yan gida ɗaya da ake zargi da kitsa garkuwar ƙarya da zummar karɓar kuɗin fansa na naira miliyan biyar a wurin mahaifinsu.
Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 17 a Borno da Adamawa Buni ya shirya bikin karrama daliban da suka lashe gasar duniyaTa bayyana cewa sun samu tushen faruwar lamarin ne bayan da wani Mista Innocent, ya kai rahoton ɓacewar ’yarsa mai shekaru 16 a ranar 18 ga Yuli, 2025.                
      
				
Mista Innocent ya shaida wa ’yan sandan cewa ’yar tasa ba ta dawo gida ba tun bayan da ta fita domin zana jarabawa a makarantar sakandare ta gwamnati da ke Karu.
Mahaifin ya bayyana cewa bayan wani lokaci ne wasu suka kira shi da waya suna neman kuɗin fansa kafin su saki ’yar tasa.
“Nan da nan DPO ɗin ofishin Jikwoyi ya ƙaddamar da bincike, inda aka bibiyi lambar wayar da aka kira da ita har aka gano cewa waɗanda suka kira suna zaune a wani gida a Jikwoyi Phase II,” in ji SP Adeh.
A cewarta, lokacin da aka isa gidan, an gano matashiyar da ake zargin an yi garkuwa da ita tare da wata mata a matsayin baƙuwa a gidan wani mai suna Mayowa Adedeji, suna cin abinci har da hira cikin natsuwa, babu wata alamar damuwa tattare da ita.
“Ƙarin bincike ya nuna cewa yayarta ce da saurayinta yayar suka shirya makircin, tare da haɗin gwiwar matashiyar da kanta,” in ji Adeh.
An gano cewa yayar matashiyar ta kista makircin da wani saurayinta, inda suka tsara yadda za su ɗauke ‘yar uwarta su ɓoye ta a gidan abokin saurayin, yayin da yayar za ta ci gaba da zama a gidan mahaifinsu domin nuna kamar ba ta da masaniya kan abin da ke faruwa.
“Ita kuwa matashiyar da aka ce an yi garkuwa da ita, ta amince da wannan shiri, kuma ta yarda za ta zauna a gidan yayin da mahaifinta ke cikin tashin hankali,” in ji sanarwar.
SP Adeh ta ce duka mutane huɗun da ake zargi suna hannun ‘yan sanda, inda nan gaba kaɗan a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala cikakken bincike.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
Jamus ta shiga sahun ƙasashen duniya da ke kiran a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da ke ci gaba da salwantar rayuka a ƙasar Sudan.
Sama da shekaru biyu ke nan Sudan na fama da yaƙin da ya ɗaiɗaita fararen hula baya ga asarar rayuka.
Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — TrumpMinistan Harkokin Wajen Jamus, Johann Wadephul, ya bayyana halin da Sudan ke ciki a matsayin “mummunan bala’i,” yana mai cewa babbar matsalar jinkai ta duniya a yanzu ta tattara ne a Sudan ɗin.
A taron da aka gudanar a Bahrain, ƙasashen Birtaniya da Jordan su ma sun yi magana kan rikicin, suna kiran da a kawo ƙarshen tashin hankalin.
A ƙarshen makon da ya gabata, RSF ta kori rundunar soji daga sansanin ta na ƙarshe a yammacin Darfur.
Rahotanni daga garin El-Fasher sun bayyana cewa ana samun kashe-kashe ba tare da shari’a ba, da fyaɗe da fashi har ma da hare-hare kan ma’aikatan agaji.
Wata Kungiyar Likitoci ta MSF a ranar Asabar ta ce ana fargabar dubban fararen hula sun maƙale sannan suna cikin mummunan haɗari a birnin Al Fasher wanda ya koma hannun dakarun RSF.
Rikicin Sudan ya fara ne a watan Afrilun 2023, bayan taƙaddama ta siyasa tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan, shugaban sojin ƙasar, da Mohamed Hamdan Dagalo (Hemedti), Kwamandan RSF.
Bayanai sun ce rikicin ya samo asali ne daga saɓani kan yadda za a haɗa rundunar RSF da sojojin ƙasar bayan juyin mulkin 2021 da ya hamɓarar da gwamnatin farar hula.
Tun daga lokacin, yaƙin ya zama wani mummunan bala’i na jin kai, inda Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta ce fiye da mutane miliyan bakwai sun tsere daga gidajensu, yayin da dubbai ke buƙatar taimakon gaggawa.