Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato
Published: 6th, August 2025 GMT
Manoma a Jihar Sakkwato sun koka game da takin da gwamnatin jihar ta ce za ta raba musu don noman damina cewa bai kai hannunsu ba.
Duk da cewa an ƙaddamar da rabon takin kusan mako guda da ya gabata.
Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a Neja Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murnaGwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya ƙaddamar da shirin sayar da takin zamani da magungunan noma a farashi mai rahusa a Ƙaramar Hukumar Gwadabawa domin bunƙasa harkar noma a daminar 2025.
Sama da buhu dubu 105 na NPK da UREA aka sayar a farashi mai rangwame.
Hakazalika, an sayi maganin kashe ƙwari da keken noma don raba wa manoma.
Sai dai manoma da dama sun ce wannan taki ba na noman damina ba ne, kuma har yanzu ba a fara rabawa ba.
Umar Yusuf, wani tsohon manomi daga Tangaza, ya ce gwamnati ta ƙaddamar da sayar da takin ne bayan damina ta kusa ƙarewa.
Kabiru Muhammad daga Kware, wanda ke da gonaki guda biyar, ya ce yana buƙatar taki amma ba a samun shi a kan lokaci.
Ya ce shirin ba ya zuwa hannun manoman gaskiya saboda ba a tsara shi yadda ya dace ba.
Muhammad Sale daga Illela ya ce ba wani manomi mai gona da ke jiran takin gwamnati, saboda duk shekara sai an makara wajen rabon taki.
Ya ce idan gwamnati ba za ta samar da taki cikin tsari ba, gara ta daina sayen shi gaba ɗaya, ta mayar da kuɗin zuwa wani aikin da zai amfani talaka da jihar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Mahara sun kashe ɗan sanda, sun ɗauke bindigarsa a Taraba
An kashe wani ɗan sanda mai muƙamin Sajan a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani shingen bincike, inda suka ɗauke bindigarsa bayan sun halaka shi a Jihar Taraba.
Wata majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a garin Tella, cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, lokacin da ’yan bindigar suka yi wa shingen binciken ƙwanton ɓauna.
An ce maharan sun harbi ɗan sandan ne a kansa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take, lamarin da ya sa sauran abokan aikinsa da ke wurin suka tsere.
Bayan sun yi kisan, ’yan bindigar sun ɗauke bindigar marigayin sannan suka tsere daga wurin.
Kakakin rundunar ’yan sandan Taraba, ASP Leshen James, bai ɗaga wayar kiran da aka yi masa ba kuma bai amsa saƙon da aka tura masa dangane da lamarin ba.