Aminiya:
2025-08-06@22:08:54 GMT

Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama

Published: 6th, August 2025 GMT

Wasu manyan jami’an gwamnati biyu a Ƙasar Ghana, sun rasu tare da wasu mutum shida a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a ranar Laraba.

Hatsarin ya faru ne a yankin Ashanti da ke Kudancin ƙasar.

Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato

Ministan Tsaro, Edward Omane Boamah, da Ministan Muhalli, Ibrahim Murtala Mohammed, na cikin jirgin soja tare da wasu fasinjoji uku da ma’aikatan jirgin guda uku.

Jirgin ya tashi daga birnin Accra, babban birnin Ghana, zuwa garin Obuasi lokacin da aka daina jin ɗuriyarsa.

Rundunar Sojin Ghana ta ce sun daina samun saƙo daga jirgin yayin da yake cikin tafiya.

Julius Debrah, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar, ya bayyana a cikin wani saƙon bidiyo cewa wannan hatsarin babban rashin ne ga ƙasar.

Ya kuma ce dukkanin tutocin ƙasar za a yi ƙasa da su har sai an bayar da sanarwa domin girmama wadanda suka rasu.

Sauran waɗanda suka rasu sun haɗa da Alhaji Mohammed Muniru Limuna (muƙaddashin mai kula da harkokin tsaron ƙasar), Samuel Sarpong (mataimakin shugaban jam’iyyar National Democratic Congress), da Samuel Aboagye (tsohon ɗan takarar majalisa).

Sunan ma’aikatan jirgin da suka mutu su ne Squadron Leader Peter Bafemi Anala, Flying Officer Malin Twum-Ampadu, da Sergeant Ernest Addo Mensah.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hatsarin jirgin sama

এছাড়াও পড়ুন:

Batun Ceto Wanda Ake Zargi Da Kwaya: Kwamishinan Kano Ya Yi Murabus

Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ke duba rawar da ya taka a batun ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.

Wannan matakin na murabus ana kallonsa a matsayin wani muhimmin cigaba da ke nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kare gaskiya, bayyana ta da kuma ɗaukar nauyin ayyukanta a bainar jama’a.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Kwamishinan ya bayyana cewa ya yanke shawarar murabus ne duba da muhimmancin al’amuran da suka shafi jama’a da kuma halin da ake ciki.

Ya ce: “A matsayina na ɗaya daga cikin masu fada-a-ji a wannan gwamnati da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, ya dace na ɗauki wannan mataki, koda kuwa zai sosa zukata.
“Ko da yake ina ci gaba da musanta hannuna a lamarin, ba zan iya watsi da irin yadda jama’a ke kallon batun ba, da kuma bukatar kare ƙimar gwamnati da muka ginata tare.” In ji shi.

Alhaji Namadi ya nuna godiya ta musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda ba shi damar yi wa jiharsa hidima, tare da jaddada aniyarsa ta ci gaba da bin manufofin gwamnatin.

Ya ƙara da cewa: “A matsayina na ɗan ƙasa nagari, dole ne in ci gaba da kare amana da hangen nesan da muka haɗa kai wajen shimfiɗawa a  jiharmu. Zan ci gaba da kasancewa mai biyayya ga akidun da suka kawo wannan gwamnati kan mulki.”

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin cikin farin ciki, tare da yi masa fatan alheri a duk wani yunƙurinsa na gaba.

Gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa wajen tabbatar da adalci, ladabi, da kuma yaki da miyagun dabi’u da laifukan da suka shafi kwayoyi da sauran matsalolin da ke shafan matasa da al’umma baki ɗaya.

Ya kuma ja hankalin duk masu rike da mukaman siyasa da su kasance masu hikima da taka-tsantsan wajen hulɗa da al’amuran jama’a, tare da neman izini daga hukumomi mafi girma kafin su shiga cikin wani lamari da ke da tasiri a bainar jama’a.

 

Abdullahi Jalaluddeen

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arziki
  • Ministan tsaron Ghana da wasu sun rasu a hatsarin jirgin sama
  • Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a Neja
  • Malaman Jami’o’in Isra’ila Sun Nemi Jamus Ta Tilasta Dakatar Da Yakin Gaza
  • Batun Ceto Wanda Ake Zargi Da Kwaya: Kwamishinan Kano Ya Yi Murabus
  • Hare-haren Boko Haram Da ‘Yan Bindiga Ya Ragu A Cikin Shekaru Biyu – Ribadu
  • Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet
  • Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura
  • Kashe N712bn Kan Gyaran Filin Jiragen Saman Legas Rashin Sanin Ya Kamata Ne – ADC