Yadda ’yan bindiga suka sace Zamfarawa 150 a cikin kwana 4
Published: 6th, August 2025 GMT
’Yan bindiga sun sace mutum 150 a mabanbantan hare-haren da suka kai kauyuka daban-daban na jihar Zamfara a cikin kwana hudu.
Kakakin Gwamnatin jihar ta Zamfara, Mahmud Mohammed Dantawasa ne ya tabbatar da hakan ga BBC.
Sai dai duk da yake bai bayyana hakikanin adadin mutanen da aka sace ba, amma ya ce gwamnatinsu na iya kokarinta wajen ganin ta ceto su.
Haka na zuwa ne a daidai lokacin da malamin addinin Musuluncin nan mazaunin Kaduna, Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunna, ya ce kwamitin zaman lafiyar da yake jagoranta ya sami nasarar kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin kasurgumin dan bindigar nan, Bello Turji, da Gwamnatin Tarayya.
Tuni dai yarjejeniyar ta kai ga sakin mutum 32 da aka yi garkuwa da su da kuma mika wasu tarin makamai ga gwamnati.
Mazauna yankunan sun ce ’yan bidnigar da ke dauke da muggan makamai ne a tsawon kwanakin suka kai hari kauyukan Sabon Garin Damri da Dakko Butsa (wanda ke da iyaka da jihar Sakkwato), da Tungar Abdu Dogo da Tungar Sarkin Daji da Sadeda da kuma kauyen Tungar Labi.
Mutanen sun ce galibi ’yan bindigar sun fi kaddamar da hare-haren ne cikin dare lokacin da mutane suke bacci, ko kuma lokacin da ake yin ruwan sama.
Kazalika, wasu majiyoyin kuma sun ce lalacewar hanyoyin jihar na taka muhimmiyar rawa wajen kara ta’azzarar hare-haren, saboda jami’an tsaro kan sha bakar wuya kafin su iya shiga yankunan su kai wa jama’a dauki cikin gaggawa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: garkuwa da mutane Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar PLA Ta Yi Sintiri A Yankin Tekun Kudancin Sin Cikin Shirin Ko Ta-Kwana
Rundunar sojin kasar Sin (PLA) ta yi sintiri a yankin tekun kudancin Sin daga ranar 3 zuwa 4 ga wata.
Kakakin rundunar PLA ta kudancin kasar Tian Junli ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin ta dauki matakin ne biyo bayan matakan Philippines na sanya kasashen dake wajen yankin cikin abun da ta kira da sintirin hadin gwiwa, wanda ke neman lalata zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin.
A cewarsa, dakarun rundunar ta kudancin kasar za su ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana da kare ikon kasar kan yankunanta da muradunta na teku ba tare da yin kasa a gwiwa ba, yana mai cewa za a dakile duk wani matakin soja dake nemen tada hankali da rikici a yankin. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp