Sin Ya Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Aiwatar Da Mataki Mai Hadari A Zirin Gaza
Published: 6th, August 2025 GMT
Da safiyar Larabar nan ne kwamitin tsaron MDD ya gudanar da taron tattaunawa game da batun rikicin Isra’ila da Falasdinu, inda a jawabinsa game da aniyar Isra’ila ta tsananta hare-haren soji, da mamaye daukacin zirin Gaza, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana matukar damuwa kan hakan, yana mai kira ga Isra’ila da ta kauracewa wannan mataki mai hadari, yana mai fatan daukacin sassan da lamarin ya shafa za su gaggauta kaiwa ga cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta mai tsorewa.
Geng Shuang, ya kuma jaddada muhimmancin aiwatar da sahihin mataki na dakatar da bude wuta yadda ya kamata, ta yadda hakan zai kubutar da rayukan al’umma, tare da bayar da damar sakin wadanda ake tsare da su, su koma ga iyalansu. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe
“Jerin sunayen yaran Gaza da ke mutuwa “, dole ne a tabbatar da ba a kara yawansu ba. Shin wadannan sunayen yara kanana da hotunan su ba za su iya tada hankalin bangarori masu rikici ba?
Akasarin kasashen duniya sun yarda cewa “shawarar samar da kasashe biyu” ita ce mafitar warware matsalar Falasdinu, kuma amincewa da kasar Falasdinu wani muhimmin mataki ne na aiwatar da wannan shawara. Kwanan nan, an gudanar da babban taron kasa da kasa kan warware matsalar Falasdinu da aiwatar da shawarar “samar da kasashe biyu” a hedkwatar MDD da ke birnin New York, inda ministocin harkokin wajen kasashe 15 suka sanya hannu kan sanarwar hadin gwiwa, suna nuna niyyar amincewa da kasar Falasdinu. A yanzu, fiye da kashi biyu bisa uku na kasashe membobin MDD sun amince da kasar Falasdinu. Muna fatan ganin an tabbatar da shawarar “kafa kasashe biyu” da wuri, domin hasken zaman lafiya ya zo Gaza. Yaran Gaza ma yara ne, kamar kowane yaro na kowane iyali a duniya, suna da hakkin rungumar gobe. (Mai zane da rubutu:MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp