Aminiya:
2025-08-05@16:25:18 GMT

Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 17 a Borno da Adamawa

Published: 5th, August 2025 GMT

Dakarun sojin Nijeriya sun hallaka aƙalla ’yan ta’adda 17 na ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a wasu hare-haren kwantan bauna da suka kai a jihohin Borno da Adamawa a tsakanin ranakun 23 ga Yuli zuwa 2 ga Agustan 2025.

Kyaftin Reuben Kovangiya, Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Buni ya shirya bikin karrama daliban da suka lashe gasar duniya An soka wa jami’in Sibil Difens wuka har lahira a Jigawa

Ya bayyana cewa sojojin ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai sun kai hare-haren ne a ƙananan hukumomin Bama, Konduga, Gwoza, Magumeri, da Biu a Jihar Borno, da kuma Michika da ke Jihar Adamawa.

A cewarsa, an kuma gano ababen fashewa 14 da ’yan ta’addan suka dasa a wurare daban-daban wadanda dakarun suka samu nasarar tarwatsa su.

“Ayyukan sun haifar da gagarumar nasara ga rundunar, inda muka hallaka mayaƙan, kuma muka ƙwato makamai da kayan yaƙi daban-daban da suke amfani da su wajen kai hare-hare,” in ji Kyaftin Kovangiya.

Kyaftin Kovangiya ya ce wannan nasara na zuwa ne bayan bincike da leƙen asiri da aka gudanar tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro da sauran hukumomin ƙasa.

Ko da yake ana samun ci gaba a fagen yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabas, amma har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da addabar sassan ƙasar, musamman a jihohin Zamfara, Katsina da wasu yankunan Borno, inda mayaƙan Boko Haram ke ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da dakarun.

Rahotanni sun nuna cewa, hare-haren ‘yan ta’adda na haifar da ƙalubale ga abinci da zaman lafiyar jama’a, musamman ga manoma da ke fuskantar barazanar kisa ko biyan haraji kafin su iya zuwa gonakinsu.

A wasu yankunan, ’yan bindiga na tilasta wa mutane biyan kuɗin kafin su shiga gona, lamarin da ke hana dubun dubatar fararen hula gudanar da harkokin noma, wanda hakan na ƙara tsananta matsin tattalin arziki da yunwa a yankunan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram ISWAP Jihar Adamawa jihar Borno

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Abdulrazaq Ya Duba Titi Mai Tsawo Kilomita 49

Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana jin dadinsa kan aikin titin Eiyenkorin zuwa Afon Ojoku zuwa Offa zuwa Odo zuwa Otin mai tsawon kilomita 49 da ake ginawa.

 

Titin siminti na daya daga cikin manyan tituna hudu da ake ba da tallafi a jihar Kwara a karkashin shirin gwamnatin tarayya na karbar haraji a misalin hadakar kamfanin BUA.

 

Gwamna AbdulRazaq ya godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da aiwatar da ayyukan karbar haraji da kuma sauran dimbin tallafin da yake baiwa jihar.

 

“Muna duba ayyukan titunan gwamnatin tarayya da na Jihohi, wannan sabon titin Ilorin/Offa ne, kuma za ku ga yadda yake da inganci, dole ne mu gode wa Shugaba Bola Tinubu kan wannan aikin hanyar, babban nasara ne kamar yadda kuke gani,” in ji shi.

 

A cewarsa aikin zai takaita lokacin balaguro tsakanin Ilorin, Offa da kuma makwabta. Lokacin da aka kammala hanyar, lura cewa lokacin tafiya zuwa Offa daga Ilorin zai kasance mintuna 30.

 

Gwamna AbdulRazaq ya ci gaba da cewa, wannan wani kyakkyawan jari ne kuma wani samfuri ne na ajandar sabunta fata, wanda ke nuna cewa manufofin suna aiki kuma akwai ƙarin kuɗi don samar da ababen more rayuwa.

 

A nasa jawabin injiniyan kamfanin dake aikin, Abdulsalam Onaolapo, ya ce suna aiki ba dare ba rana domin kamala aikin akan lokaci.

 

 

COV/ALI MUHAMMAD RABIU

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA
  • Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara
  • Gwamna AbdulRazaq Ya Amince Da Naira Biliyan 20 Don Gyaran Gine-ginen Makarantu A Kwara
  • Gwamna Abdulrazaq Ya Duba Titi Mai Tsawo Kilomita 49
  • An kama dilallan ƙwaya 28 a cikin barikin sojoji a Kaduna
  • Amurka Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Zuwa Ƙasarta Domin Haihuwa
  • Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba
  • Borno Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijira 5,000 Kafin Damuna Ta Kare
  • Ambaliya: Mutum 165 sun mutu a Nijeriya a bana — NEMA