Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Wajabcin Haduwar Kasashen Musulmi Wajen Hana Laifukan Gaza
Published: 6th, August 2025 GMT
Shugaban Kasar Iran ya jaddada cewa; Dole ne kasashen musulmi su hana ci gaba da aikata laifuka a Gaza
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da fira ministan Malaysia Anwar Ibrahim, ya jaddada bukatar kasashen musulmi su dauki matakin hana ci gaba da bala’in jin kai a Gaza ta hanyar diflomasiyya da kuma matsin lamba na siyasa.
A safiyar yau Laraba ne shugaba Pezeshkian ya tattauna da fira ministan Malaysia Anwar Ibrahim ta wayar tarho, inda ya jaddada cewa: “Aikin ta’addancin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta aiwatar a Gaza ba abin da za a amince da shi ba ne ga kowane mai ‘yanci,” yana mai bayyana fatansa na ganin “kasashen Musulmi za su yi aiki tare da hadin kai, ta hanyar diplomasiyya mai inganci, don hana ci gaba da wadannan laifuka.”
Pezeshkian ya kuma kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance mai kare hakkin al’ummar Falastinu da ake zalunta, inda ta yi kira ga sauran kasashen musulmi da su kara daukar matakai masu tsauri da tasiri wajen nuna goyon baya ga Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Taya Ali Larijani Murnar Nada Shi Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran August 6, 2025 An Fara Gudanar Da Juyayin Cikan Shekaru 80 Da Harin Amurka Da Makamin Nukiliya Kan Hiroshima Na Kasar Japan August 6, 2025 Dakarun Kai Daukin Gaggawa Na Sudan Sun Kashe Fararen Hula 14 Tare Da Jikkata Wasu Na Daban August 6, 2025 IRGC: Bayan yakin Kwanaki 12 Yanayi Ya Sauya Zuwa Ga Amfani Ga Iran August 6, 2025 ‘Yansanda A Iran Suna Amfani Da Kayakin Tsaro Na Zamani A Lokacin 40 August 6, 2025 Iran tana Goyon Bayan Zaman Lafiya Tsakanun Kasashen Yankin August 6, 2025 Iran Ta Ce Babu Wani Da Zai Kusanci Cibiyoyin Tashe Makamashin Uranim Na Kasar August 6, 2025 Iran: Yakin Kwanaki 12 Ya Bayyana Inganci Da Karfin Yakin Yanar Gizo Na Kasar August 6, 2025 Iran: An nada Larijani a matsayin sakataren kwamitin koli na tsaron kasa August 6, 2025 Sheikh Qassem: Tsaron Isra’ila zai rushe cikin sa’a 1 idan ta shelanta yaki a kan Lebanon August 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugabannin Iran Da Faransa Sun Yi Wata Tattaunawa Ta Wayar Tarho
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bukaci Amurka da Turai su nuna gaskiya idan suna son sake gina aminci da Iran.
A wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, da takwaransa na Iran Mas’ud Pezeshkian, shugaban na Iran ya ce dole ne turai su mutunta ‘yancin Iran kuma su daina gabtar da bukatu da Iran ba za ta taba amincewa da su ba.
Iran ta yi maraba da tattaunawa amma Pezeshkian ya sake nanata cewa, a yanzu ba Iran ce za ta tabbatar da gaskyarta ba, domin ta riga ta yi haka, ya rage kan kasashen turai ne su tabbatar wa duniya cewa da gaske suke yi a cikin abin da suke furtawa.
Duk da haka, ya ce, Iran na ci gaba da fuskantar zarge-zarge marasa tushe da kuma ƙarin takunkumi a ƙarƙashin hujjar cewa tana hankoron kera mkaman nukiliya.
Pezeshkian ya jaddada cewa za a iya magance matsaloli ne kawai ta hanyar tattaunawa da mutunta juna, ba ta hanyar tilastawa ko barazana ba.
“Inda za a iya magance rashin fahimta ta hanyar yin amfani da hankali, me ya kawo maganar yin amfani a karfi da kashe-kashe da rusa gine-gine da ababen mor rayuwa na al’ummar kasa.
A nasa bangaren, Macron ya gode wa Pezeshkian saboda matakan da aka dauka don aiwatar da yarjejeniyoyin da suka gabata kuma ya bayyana niyyarsa ta yin aiki don samar da sabon tsari na tattaunawa tsakanin Iran da kasashen Yammacin duniya.
Ya ce ci gaba da tattaunawa yana da mahimmanci don gina gaskiya da aminci, da dage takunkumi, da kuma inganta dangantakar kasashen biyu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya Ta Sake Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar November 6, 2025 Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya November 6, 2025 Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba November 6, 2025 Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya November 6, 2025 An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bisa Tuhumar Fitar Da Bayanai Na Hukuma November 5, 2025 Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar UAE Da Taimakon Rundunar RSF November 5, 2025 Shugaban Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci