NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma
Published: 7th, August 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A cewar masana harkar kiwon lafiya, rashin tantancewa balle a bayar da kulawar da ta dace a kan lokaci na cikin dalilan ta’azzarar barazanar da Zazzabin Lassa ke yi ga bangarori da dama na rayuwar al’ummar Najeriya, musamman a yankunan karkara.
Wani bincike a kan tasirin Zazzabin Lassa a kan rayuwar ‘’yan Najeriya wanda aka wallafa bara a mujallar Springer ya nuna gudunmawar da jahilci yake taimakawa wajen yaduwar cutar a kasar.
A sassan Najeriya da dama dai, ba kasafai mutane ke iya bambance Zazzabin Lassa da sauran nau’ukan zazzabi ba.
Shin yaya za a iya gane Zazzabin Lassa a kuma bambance da sauran nau’ukan zazzabi? NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya Karu DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani?
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hukumar Yaki da Cutuka Masu Yaduwa NCDC
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisa ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a Bauchi
Majalisar Dokokin Bauchi ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a fadin jihar domin haɓaka ci gaba, inganta shugabanci, da kawo sauƙin gudanar da mulki.
Wannan na ƙunshe ne a wani ƙudiri da dan majalisar mai wakiltar mazabar Disina, Sale Hodi Jibir, ya gabatar a yayin zaman da Kakakin Majalisar, Abubakar Y. Sulaiman, ya jagoranta.
Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arziki Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin samaA cewar Jibir, ƙudurin yana dogaro ne da tanadin kundin tsarin mulki na 1999 wanda ya bai wa majalisun dokokin jihohi damar fara shirin ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi, matuƙar an cika wasu sharuɗa da suka haɗa da goyon bayan kashi biyu bisa uku na mambobin majalisa, da mincewar ƙananan hukumomin da abin ya shafa da kuma gudanar da zaɓen raba gardama.
Jibir ya bayyana cewa ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi zai sauƙaƙa rarraba albarkatu cikin adalci da inganta shugabanci da gudanarwa a matakin ƙasa da ƙarfafa haɗin kan al’umma da ci gaban tattalin arziki.
Ya kuma ce yankuna da dama a Jihar Bauchi sun gabatar da buƙatar a ware musu ƙaramar hukuma, musamman duba da girman yankunansu, yawan al’umma, bambancin al’adu da kuma ƙalubalen gudanar da mulki.
Jibir ya buƙaci a kafa kwamitin wucin gadi na musamman domin tattarawa da tantance buƙatun al’umma, da tuntuɓar sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da nazarce-nazarce kan fadin ƙasa, da yawan jama’a da yanayin tattalin arziki na yankunan da ake neman a samar musu da ƙananan hukumomi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ƙudirin wanda ya samu goyon bayan wasu mambobin majalisar da suka buƙaci a gaggauta aiwatar da shi domin amfanin jama’a sun haɗa da Jamilu Umaru Dahiru da Musa Wakili Nakwada da Ibrahim Tanko Burra da Sa’idu Sulaiman Darazo da Dokta Nasiru Ahmed Ala.
A wani ɓangare na zaman, majalisar ta amince da rahoton kwamitinta na ma’aikata, dangane da ƙorafe-ƙorafen rashin biyan ’yan fansho da albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi a faɗin jihar.