Kungiyar Hamas Ta Sanar Da Shirin Sakin Dukkanin Fursunonin Isra’ila Bisa Sharuddan Da Ta Gindaya
Published: 15th, April 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar da sharudan sakin dukkan fursunonin Isra’ila da take tsare da su
Wani jami’in Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya ce: Kungiyar a shirye take ta sako daukacin fursunonin Isra’ila domin tsagaita bude wuta da ficewa daga Gaza, kamar yadda wani rahoto da tashar talabijin ta Alkahira ta fitar.
Jami’in na kungiyar Hamas ya kara da cewa: A ranar litinin din nan ne haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma yin watsi da alkawurran da ta dauka, yana mai cewa kungiyar Hamas ta tabbatar wa masu shiga tsakani da “bukatar bayar da lamuni don tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila aiwatar da yarjejeniyar.”
Yana mai bayyana cewa, “Hamas ta yi aiki mai kyau kuma tare da babban sassauci gami da aiki da ra’ayoyin da aka gabatar mata a cikin shawarwarin tsagaita wuta da musayar fursunonin Isra’ila.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mujallar “Foreign Policy”Ta Amurka: Isra’ila Ba Ta Yi Nasara A Yaki Da Iran Ba
Jaridun kasar Amurka sun bayyana cewa; Isra’ila ta kasa cimma manufofin da ta ayyana a yaki da Iran, sannan kuma ta kara zama saniyar ware a duniya.
Mujallar “Foreign Policy” ta yi ishara da sakamakon yakin da take cewa, ya zamarwa Amurka da kawarta Isra’ila juyewar reshe da mujiya,domin harin da su ka kai wa Shirin Iran na Nukiliya bai iya kawo karshensa baki daya,maimakon haka ma sai ya jazawa Tel Aviv asarar mai yawa da kuma karfafa kishin kasa a tsakanin Iraniyawa.”
Har ila yau, rahoton mujallar ta “”Foreign Policy” ya ci gaba da cewa; Asarar da aka yi a Isra’ila, tana firgitarwa”,amma a cikin Iran babu cikakken bayani akan girman barnar da aka yi- da hakan yake a matsayin tsaka mai yuwa ta fuskar muhimman manufofin da Isra’ilan ta so cimmawa da kuma kawarta Amurka.”
Bugu da kari mujallar ta “Foreign Policy” ta ce; Babu wanda yake gaskata abinda Isra’ila take fada na cewa ta rusa Shirin makamashin Nukiliyar Iran,domin hukumomin leken asiri na turai suna cewa, dukkanin sanadarorin kera makaman Nukiliya suna nan kalau ba abinda ya same su.”
Wani sashe na rahoton ya ce; HKI ba ta iya samar da kandagarko na Nukiliya a yakinta da Iran ba,maimakon hakan ma, abu ne mai yiyuwa harin da Isra’ilan da Amurka su ka kai wa Iran ya ba ta karfin gwiwar yin tunanin samar da makamin Nukiliya” a fadar wannan mujalla.
Iran dai ta sha bayyana cewa; Shirinta na sulhu ne, ba kuma wanda yake da hakkin hana ta cin moriyar alfanu mai yawa dake cikin fasahar makamashin Nukiliya.
Rahoton ya kuma ce; gwamnatin Amurka ta fake da dalilai na karya wajen kai wa Iran hari.