Aminiya:
2025-09-19@23:35:21 GMT

An soka wa jami’in Sibil Difens wuka har lahira a Jigawa

Published: 5th, August 2025 GMT

Wasu zauna gari banza sun burma wa wani jami’in Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) wuka har lahira a Kasuwar Shuwarin da ke ci Karamar Hukumar Kyawa a Jihar Jigawa.

Kakakin Hukumar NSCDC reshen Jihar Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani, ya bayyana cewa an kai wa jami’in hari ne a lokacin da yake bakin aiki a ranar Linitin a lsashin sayar da shanu na kasuwar (Kara), inda ’yan iskan suka kai wa jami’in hari.

Ya ce “Maharan da ake zargin suna xauke da wuqaqe ne suka farma   jami’in, suka yi masa mummunar varna, inda maharan suka far wa jami’in da wukake, kuma abin takaici, ya rasa ransa nan take.

Kakakin ya bayyana cewa, “Wanda abin ya shafa mai suna Sufeto Bashir Adamu Jibril, ma’aikaci ne a sashin bincike na hukumar NSCDC ta jihar Jigawa.

Majalisa ta amince da sabuwar Dokar Masarautun Katsina Ɗaliba ’yar shekara 15 daga Yobe ta lashe Gasar Muhawara ta Duniya

An garzaya da shi zuwa babban asibitin Dutse inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa, kuma an kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da wasu da dama kuma suka gudu.

Rundunar ta yi Allah wadai da lamarin tare da tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci.  “Za mu tabbatar an gurfanar da wadanda suka aikata wannan danyen aiki a gaban kotu”, in ji Tijjani.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: bata gari Zauna gari banza

এছাড়াও পড়ুন:

An kama sojan bogi da ɓarayin mota 2 a Jigawa

Rundunar ‘yan Sandan Jihar Jigawa ta bada sanarwar nasarar cafke wani sojan bogi da ƙarin wasu mutum biyu da ake zargi da satar mota a ƙauyen Sabon Sara.

Kamar yadda Kakakin rundunar ’yan sanda na Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam ya sanarwa manema labarai a garin Dutse cewa, an kama matashin sojan bogin da abokansa da ake zargin su da satar mota a ƙauyen Sabon Sara, cikin ƙaramar hukumar Kafin Hausa.

Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya

A cewar majiyar an kama sojan bogin mai suna Kabiru Musa da abokan aikinsa Umar Ali da Sabi’u Bashir, dukkansu ‘yan asalin Jihar Kano.

A cewar kakakin rundunar waɗannan mutane an kuma same su da katin cire kuɗi ATM guda 7, lasisin tuƙi guda biyu da kuma sauran kayan da su ke amfani da su wajen aikata laifin da suka ƙunshi kakin sojan da shi Kabiru Ali ke amfanin da shi.

“Da zarar an kammala bincike za a miƙa su gaban kuliya don fuskantar abin da suka aikata.”in ji SP Lawan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Alhazai Ta Jigawa Za Ta Shirya Taron Bita Na Musamman Ga Jami’anta
  • Hukumar Bunkasa Ilimin Manyan Makarantu Ta Shirya Taro Na Musamman Ga Jami’anta
  • An kama sojan bogi da ɓarayin mota 2 a Jigawa
  • An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda
  • ‘Yansan Jigawa Sun Tabbatarwa Mafarauta Da ‘Yan Bulala Samun Horo
  • Mataimakin Gwamnan Zamfara Ya Jajantawa Al’ummar Gumi
  • Gobara ta kashe manyan jami’an hukumar FIRS 4 a Legas
  • UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna