Gwamnatin Kano Za Ta Farfado Da Makarantu Tare Da Kara Inganta Fannin Ilimi
Published: 6th, August 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudurinta na farfado da harkar ilimi ta hanyar gyara makarantun da suka lalace wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata.
Da yake jawabi yayin wata ziyarar duba makarantu a Makarantar Sakandare ta Murtala Muhammad da ke ƙaramar hukumar Tarauni, Kwamishinan Ilimi, Dr.
Kwamishinan ya nuna damuwa game da yadda ake amfani da harabar makarantu ba bisa ka’ida ba, musamman yadda wasu mazauna yankunan suka mayar da harabar Makarantar Murtala Muhammad wajen zubar da shara.
Ya tabbatar da cewa za a ɗauki matakin gaggawa don dakile lalacewar muhalli da kuma tabbatar da amintaccen wuri don karatu.
Yayin zagayen nasa, Dr. Makoda ya kuma kai ziyara zuwa Makarantar Sakandare ta ‘Yan Mata da ke Guringawa, inda ya duba aikin gine-gine da gyare-gyare da ke gudana.
Ya yaba da jajircewar ɗan kwangilar wajen cika aikin cikin lokaci da kuma bin ƙa’idojin aikin.
Aikin ya haɗa da gine-ginen bene biyu masu ɗakunan karatu huɗu kowanne, bandakunan ɗalibai da na malamai, da ofisoshin malamai, da gina katangar makarantar da kuma rijiyar burtsatse don samun ruwan sha mai tsafta.
Kwamishinan ya kuma kai ziyara zuwa Makarantar Sakandare ta Tukun Tawa, wacce aka gyara a baya ƙarƙashin shirin 484 Ward Project na jihar, wanda ke karkashin jagorancin ƙananan hukumomi. Ya bayyana wannan a matsayin misali na ci gaba daga matakin ƙasa a fannin ilimi.
Ya jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf yana nan daram da alkawarin da ya ɗauka na samar da ingantaccen ilimi ga kowanne yaro a Jihar Kano.
Idan za a iya tunawa, a baya Gwamnatin Kano ta amince da kashe biliyoyin naira domin sauya fasalin ilimi da inganta gine-ginen makarantu.
Khadijah Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamitin Binciken Ya Kammala Rahoto Kan Kwamishinan Sufuri Ga Gwamnatin Kano
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp