Aminiya:
2025-11-08@18:23:57 GMT

Ministan tsaron Ghana da wasu sun rasu a hatsarin jirgin sama

Published: 6th, August 2025 GMT

Wasu manyan jami’an gwamnati biyu a Ƙasar Ghana, sun rasu tare da wasu mutum shida a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a ranar Laraba.

Hatsarin ya faru ne a yankin Ashanti da ke Kudancin ƙasar.

Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato

Ministan Tsaro, Edward Omane Boamah, da Ministan Muhalli, Ibrahim Murtala Mohammed, na cikin jirgin soja tare da wasu fasinjoji uku da ma’aikatan jirgin guda uku.

Jirgin ya tashi daga birnin Accra, babban birnin Ghana, zuwa garin Obuasi lokacin da aka daina jin ɗuriyarsa.

Rundunar Sojin Ghana ta ce sun daina samun saƙo daga jirgin yayin da yake cikin tafiya.

Julius Debrah, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar, ya bayyana a cikin wani saƙon bidiyo cewa wannan hatsarin babban rashin ne ga ƙasar.

Ya kuma ce dukkanin tutocin ƙasar za a yi ƙasa da su har sai an bayar da sanarwa domin girmama wadanda suka rasu.

Sauran waɗanda suka rasu sun haɗa da Alhaji Mohammed Muniru Limuna (muƙaddashin mai kula da harkokin tsaron ƙasar), Samuel Sarpong (mataimakin shugaban jam’iyyar National Democratic Congress), da Samuel Aboagye (tsohon ɗan takarar majalisa).

Sunan ma’aikatan jirgin da suka mutu su ne Squadron Leader Peter Bafemi Anala, Flying Officer Malin Twum-Ampadu, da Sergeant Ernest Addo Mensah.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hatsarin jirgin sama

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa

Gwamnatin Tarayya ta ce ƙofofinta buɗe suke ta sayar da dukkan matatun manta na Warri, Fatakwal da Kaduna ga ’yan kasuwa domin ƙarfafa gasa a fannin tace mai a Najeriya.

Mai ba Shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana hakan a wata hira da Bloomberg TV a gefen taron makamashi na ADIPEC da aka gudanar a Abu Dhabi, Hadaddiyar Daular Larabawa, ranar Talata.

Hafsan sojin sama ya umarci a yawaita yi wa ’yan ta’adda ruwan bama-bamai NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir

Verheijen ta ce wannan mataki na daga cikin shawarwarin da ake dubawa don inganta harkar man fetur a Najeriya.

“Daya daga cikin matakan da za a iya la’akari da su kenan, musamman idan aka samu wanda yaje da kwarewa da kuma jarin da zai iya sayen su,” in ji ta.

Ta ce matatun man da a baya suka dade suna aiki a ƙarƙashin tallafin gwamnati, yanzu sun sami kishiyoyi bayan cire tallafin man fetur.

“Yanzu da muka cire tallafin, mun kawar da duk wani tarnaki da ke cikin wannan kasuwar ta man fetur,” kamar yadda ta fada.

A watan Oktoba, Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) Limited ya sanar da fara cikakken bincike na fasaha da kasuwanci kan matatun mai guda hudu da gwamnati ke da su.

Tun a watan Yuli, Shugaban kamfanin Group, Bayo Ojulari, ya ce aikin gyaran matatun ya ɗan samu tsaiko, yana mai cewa kamfanin na fatan kammala sake duba su kafin ƙarshen shekara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja
  • Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano
  • Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho
  • Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800
  • Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya
  • An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8
  • Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro
  • Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa
  • Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos
  • Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu