Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arziki
Published: 6th, August 2025 GMT
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da kyautar fuloti da kuɗi naira miliyan biyar ga kowane ɗaya daga cikin iyalan tawagar ’yan wasan nan na Kano 22 da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya auku a watan Yuni.
Mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya tabbatar da wannan kyauta cikin wani saƙo da ya wallafa a Facebook a wannan Larabar.
“Mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa iyalan ’yan wasan da suka rasu fuloti ɗaya da kuma naira miliyan biyar kowannensu,” in ji sanarwar.
Aminiya ta ruwaito cewa, tawagar ’yan wasan da suka rasu ta yi hatsari ne a yayin da suke dawowa daga gasar wasannin ƙasa ta National Sports Festival da aka gudanar a Jihar Ogun.
Tawagar da lamarin ya rutsa da ita ta ƙunshi ’yan wasa, masu horarwa, mataimakansu, jami’an lafiya, direbobi, injiniyoyi da kuma ɗan jarida.
Ajali ya katse musu hanzari ne bayan samun nasarori daban-daban a gasar ta National Sports Festival da suka haɗa da sarƙoƙin zinare 6, azurfa 13 da na tagulla 10 da suka lashe.
Ana iya tuna cewa, mummunan lamarin ya auku ne a garin Dakatsalle da ke ƙaramar hukumar Bebeji, kimanin kilomita 50 daga Kano, a yayin da ya rage ƙiris tawagar ta ƙarasa gida.
Tun a wancan lokaci, jama’a daga ciki da wajen Jihar Kano suka riƙa jimami da bayyana alhini, musamman duba da irin gudummawar da ’yan wasan suka bayar kafin rasuwarsu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan wasa Hatsari Jihar Kano da suka rasu
এছাড়াও পড়ুন:
Genoa ta naɗa Daniele De Rossi sabon kociya
Kungiyar Genoa ta naɗa tsohon ɗan wasan tsakiyar Italiya, Daniele De Rossi, a matsayin sabon kociyarta, domin maye gurbin Patrick Vieira wanda ya bar ƙungiyar a ƙarshen mako.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Genoa ta bayyana cewa tana “maraba da Daniele De Rossi” wanda ya jagoranci atisaye na farko da yammacin wannan ranar. Za a gudanar da taron manema labarai na farko da shi a ranar Juma’a.”
Victor Osimhen ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a Champions League Ajax ta kori kocinta John HeitingaDe Rossi, wanda ya taka leda na tsawon shekaru 17 a Roma kuma ya lashe Kofin Duniya tare da Italiya a 2006, ya taɓa horas da ƙungiyoyin Spal da Roma.
Roma ce ƙungiyar da De Rossi ya kai zuwa wasan kusa da na ƙarshe a gasar Europa League ta 2024, kafin a sallame shi bayan rashin nasara a wasanni hudu a jere a kakar da ta biyo baya.
A makon da ya gabata, Genoa ta kuma sallami daraktan wasanninta Marco Ottolini, inda ta maye gurbinsa da ɗan ƙasar Sifaniya, Diego Lopez.