Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina
Published: 6th, August 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargaɗi maƙarrabansa cewa duk wanda ba zai iya sauke nauyin da aka ɗora masa, ya yi murabus.
Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan murabus ɗin Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi, ya yi biyo bayan belin wani da ake zargin dilan miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Danwawu.
Wannan lamari ya tayar da ƙura, wanda hakan ya sa Gwamna Abba, ya ɗauki mataki.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya bayyana rashin jin daɗinsa kan lamarin.
Hakan ta sa ya jaddada buƙatar dukkanin mambobin majalisar da sauran manyan jami’an gwamnati su kasance masu gaskiya da riƙon amana.
“Ba za mu lamunci kowace irin ɗabi’a ta ƙashin kai da za ta ci gaba da lalata ƙimar gwamnatinmu ba,” in ji Gwamnan.
“Dukkanin ma’aikata dole su kasance masu lura da kuma ɗaukar nauyin ayyukansu. Ba ofishinku kawai kuke wakilta ba, kuna wakiltar gwamnatinmu.”
Gwamnan ya ƙara da cewa duk wanda ba zai iya sauke nauyin amanar da aka ɗora masa ba, ya yi murabus da kansa maimakon aikata wani abu da zai ɓata sunan gwamnati.
Ya kuma nanata cewa yaƙi da miyagun ƙwayoyi da sauran munanan ɗabi’u a cikin al’umma yana daga cikin ginshiƙin mulkinsa.
Ya ce duk wanda aka samu yana da hannu kai-tsaye ko a kaikaice wajen taimaka wa masu aikata irin waɗannan laifuka, zai fuskanci hukunci.
“Mun hau mulki da kyakkyawan manufa ta daidaita al’amura, gaskiya da ci gaba a Jihar Kano. Wannan buri ba zai taɓa taɓewa ba,” in ji shi.
Wannan mataki da gwamnan ya ɗauka na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ke ƙara barazana ga matasa da zaman lafiyar al’umma a jihar.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da adalci, gaskiya da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar Jihar Kano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gargadi Ibrahim Namadi Kwamishina Miyagun ƙwayoyi
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Yusuf Ya Kaddamar da Shirin Dashe Itatuwa Don Yaki da Matsalolin Muhalli
Gwamnatin Jihar Kano ta sake tabbatar da kudurinta na yaki da zaizayar ƙasa, ambaliyar ruwa, da sauran matsalolin da suka shafi muhalli.
Wannan bayani ya fito ne daga Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin kaddamar da babban shirin dashen itatuwa da za a shuka tsirrai miliyan biyar da rabi a faɗin jihar, wanda aka gudanar a ƙaramar hukumar Makoda.
Ya bayyana cewa babban burin wannan shiri shi ne magance dimbin matsalolin muhalli da ke addabar al’ummar Kano.
Gwamna Yusuf ya jaddada cewa waɗannan matsaloli sun jawo manyan kalubale ga al’umma.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta samar da dukkan kayayyakin da suka wajaba don kula da tsirran da za a dasa, domin su girma yadda ya kamata tare da cika manufarsu. Wannan goyon baya na da matuƙar muhimmanci wajen nasarar shirin.
Ya bukaci dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 44, sarakuna da jami’an raya al’umma da su shiga cikin wannan shiri, yana mai cewa halartar su na da matuƙar amfani wajen cimma burin da aka sa gaba.
“Idan aka kula da itatuwan da kyau, za su taka muhimmiyar rawa wajen rage sauyin yanayi da sauran matsalolin da suka shafi muhalli. Wannan na cikin manyan manufofin muhalli na Jihar Kano.” In ji shi.
Kwamishinan Muhalli, Dr. Dahiru Mohammad Hashim, ya yabawa Gwamna Yusuf bisa goyon bayan da yake bai wa ma’aikatar don yaki da matsalolin muhalli.
Wakilin Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II, wato Sarkin Dawakin Mai Tuta Alhaji Mohammad Bello Abubakar, ya sake jaddada goyon bayan masarautar ga wannan shirin na dashen itatuwa.
A yayin taron, an gabatar da kyaututtuka ga wasu mutane da suka taka rawar gani wajen tallafawa al’ummominsu.
Wannan karramawa na matsayin kwarin gwiwa ne ga wasu domin su shiga irin waɗannan ayyuka na kula da muhalli.
Abdullahi Jalaluddeen