Yunkurin Netanyahu na mamaye Gaza ya tayar da balli a Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Published: 6th, August 2025 GMT
A wata ganawa da ya yi da manyan jami’an tsaro a wannan Talata don kammala dabarun yakin Gaza, Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da kwace yankin zirin Gaza baki daya da karfin soji, duk da hadarin da ke tattare da sauran fursunonin yahudawa da ke tsare a hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa a Gaza.
Ofishin Netanyahu ya fitar da wata ‘yar gajeriyar sanarwa da ke tabbatar da cewa Netanyahu ya gudanar da wani zaman shawarwarin tsaro na tsawon sa’o’i uku, inda babban kwamnadan rundunar sojojin Isra’ila ya bayyana yuwuwar aiwatar da Shirin mamaye zirin yakin Gaza baki. Sanarwar ta kara da cewa rundnar sojin Isra’ila ashirye take domin aiwatar da duk wani matakin da majalisar tsaron kasa ta dauka.
Majiyoyin yada labarai na Haramtacciyar Kasar Isra’ila da dama sun ruwaito cewa taron ya nemi kammala shawarwarin da majalisar ministoci ta a karshen wannan mako.
Zaman taron na wannan Talata ya hada da ministan yakin Isra’ila Katz, ministan kula da tsare-tsare Ron Dermer, da kuma shugaban hukumar gudanarwa ta rundunar soji Maj. Gen. Itzik Cohen. A halin da ake ciki, ministan ‘yan sanda mai tsattasauran ra’ayi Itamar Ben-Gvir da ministan kudi Bezalel Smotrich, dukkansu sun nuna cikakken goyon bayansu ga Shirin mamaye zdaukacin yankin zirin Gaza, kamar yadda jaridar Isra’ila Hayom ta ruwaito.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa kafar yada labarai ta Kan bayan taron cewa, Netanyahu na matukar goyon bayan mamayar Gaza, kamar yadda rahotannin da suka fito daga kafafen yada labarai na Isra’ila Ynet da i24 News suka ambata.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqch: Hadin Kai Tsakanin Cibiyoyi Na Tabbatar Da Karfi Da Ci Gaba August 5, 2025 Wilayati: Iran Ba Za Ta Amince Da Yin Amfani Da Hanyar Zangezur Ta Hanyar Da Bata Dace Ba August 5, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Da Ke Yankin Jaffa Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 5, 2025 Dr Muhammad Tahir Da Aka Yi Wa Barazanar Kisa Ya Bayyana Abin Da Ya Gani Na Masifa A Gaza August 5, 2025 An Samu Bullar Sabani Da Rikici Tsakanin ‘Yan Sahayoniyya Game Da Batun Mamaye Zirin Gaza August 5, 2025 Jiniyoyin Gargadi Sun Tashi A HKI Bayan Da Yemen Ta Cilla Sabbin Makamai August 5, 2025 Iran Ta Kafa Kwamitin Tsaron Kasa Wanda Zai Kula Da Sabbin Matsalolin Tsaro August 5, 2025 Rasha Zata Kara Kyautata Dangantaka BRICS don Magance Takunkuman Amurka A Kanta August 5, 2025 Gagarumar Zanga-Zang A birnin Paris Na kasar Faransa Saboda Killace Gaza August 5, 2025 Burtaniya Zata Fara maida yan Gudun Hijira Zuwa Faransa Bisa Wata Sabuwar Yarjeniya August 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Haramtacciyar Kasar Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya musanta zargin da y ace karce ce ” da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta yi cewa Hamas ta sace wata babbar mota dauke da kayan agaji.
“Mun tabbatar da cewa wannan zargin karya ne, kuma wani bangare ne na manufar kafofin watsa labarai da nufin bata sunan rundunar ‘yan sandan Falasdinu, wadanda ke aikinsu na kasa da na jin kai na neman taimako da kare ayarin motocin agaji,” in ji Ismail Al-Thawabta, darektan ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza.
Yakara da cewa ba a fayyace ainihin rana, lokaci, da wurin da lamarin ya faru ba, Al-Thawabta ya bayyana bidiyon a matsayin “yunkuri bayyananne na yada bayanai marasa tushe.”
Sanarwar ta karyata ikirarin CENTCOM cewa “kusan kasashe 40 da kungiyoyin kasa da kasa suna aiki a Gaza,” yana mai jaddada cewa ainihin adadin kungiyoyin da ke ba da agajin jin kai bai wuce 22 ba, “yawancinsu suna fama da cikas da kuntatawa saboda matakan da gwamnatin mamayar Isra’ila ta sanya.”
Haka kuma ta soki shiru da CENTCOM ta yi game da laifuka da cin zarafi da Isra’ila ke yi a kullum tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.
“Shirun da rundunar sojin Amurka ta yi a gaban wadannan laifukan na yau da kullum, yayin da take aiki don yada labaran da ba su da tushe game da rundunar ‘yan sandan Falasdinu, ya nuna cikakken son kai ga mamayar Isra’ila da kuma rashin sahihancinta a matsayin wacce ya kamata ta kasance mai shiga tsakani,” in ji sanarwar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci