Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murna
Published: 6th, August 2025 GMT
Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya taya daliban nan ’yan mata ‘yan asalin jihar Yobe su uku da suka lashe gasar harshen Turanci da aka yi a birnin Landan na Burtaniya.
A farkon makon nan ne dai Nafisa Abdullahi Aminu da Rukayya Muhammad Fema da kuma Hadiza Kashim Kalli suka zama zakaru a gasar TeenEagle ta 2025 da aka yi a birnin na Landan.
A cikin wata sanarwa daga bakin kakakinsa, Bayo Onanuga, ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya ce nasarar ’yan matan abin alfahari ce ga Najeriya.
Tinubu ya kuma yaba wa makarantun da daliban suke karatu, inda ya ce nasarar daliban wata alama ce ta kyau da ingancin karatun Najeriya da suke samar da hazikan dalibai da duniya ke alfahari da su.
Shugaban ya kuma yaba wa daliban tare da shawartar su da su ci gaba da mayar da hankali a kan karatunsu, sannan ya yi musu fatan nasara a rayuwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gasar Turanci
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025
Rahotonni Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna November 8, 2025
Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025