Sashen Cinikayyar Samar Da Hidimomi Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso Takwas A Rabin Farko Na Shekarar 2025
Published: 5th, August 2025 GMT
Sashen cinikayyar samar da hidimomi na Sin ya ci gaba da bunkasa yadda ya kamata cikin watanni shida na farkon shekarar nan ta 2025, inda ya karu da kaso takwas bisa dari kan mizanin shekara. A cewar ma’aikatar cinikayya ta Sin, darajar hidimomin shige da fice a wannan wa’adi ta kai kudin Sin tiriliyan 3.                
      
				
Cikin wannan adadi, alkaluman hidimomin da aka fitar daga kasar Sin ya karu da kaso 15 bisa dari, wato darajar da ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 1.69, yayin da na wadanda aka shigo da su kasar ya karu da kaso 3.2 bisa dari, daidai da kudin Sin tiriliyan 2.2. Sai kuma gibin cinikayya a fannin na bayar da hidimomi da ya ragu da yuan biliyan 152.2, idan an kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar bara.
Hidimomin da suka kunshi ilimi mai zurfi na ci gaba da samun ci gaban cinikayya, inda fannin shige da ficensu ya karu da kaso shida bisa dari a mizanin shekara, kana darajarsu ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 1.5.
Hidimomin tafiye-tafiye ne kan gaba a wa’adin na watanni shida, inda suka samu karuwar kaso 12.3 bisa dari a mizanin shekara, da darajar kudin Sin yuan tiriliyan 1.08. Kazalika, fannin hidimomin tafiye-tafiye da aka samar ga sassan ketare ya karu da kaso 68.7 bisa dari a wa’adin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ya karu da kaso
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar
Daga Usman Mohammed Zaria
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Injiniya (Dr.) Muhammad Uba, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa amincewa da sabbin ayyukan gina hanyoyi a fadin jihar, ciki har da na Birnin Kudu.
Ya ce wannan mataki na cikin ajandar gwamnati 12, musamman wajen inganta ci gaban ababen more rayuwa.
A cewarsa, Birnin Kudu za ta amfana da gina hanyoyi masu tsawon kilomita 113, wanda ya hada da hanyoyin kauyuka da wadanda ke hada al’umma da sauran sassan jihar.
Dr. Uba ya bayyana aikin a matsayin babban ci gaba wajen saukaka zirga-zirga, inganta harkokin tattalin arziki da samun sauki ga muhimman ayyuka ga jama’a.
Ya bayyana tabbacin cewa za a dade ana cin moriyar aikin hanyoyin, tare da hanzar ayyukan ci gaba da bunkasar karamar hukumar.
Shugaban ya yi addu’ar dorewar zaman lafiya da cigaba a Birnin Kudu tare da yin alkawarin ci gaba da hada kai da gwamnatin jiha domin tabbatar da cewa jama’a suna amfana da fa’idodin dimokuraɗiyya.