‘Za a yi ambaliyar kwana 5 a jihohi 19 na Najeriya’
Published: 6th, August 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen cewa za a tafka mamakon ruwan sama na tsawon kwana biyar da zai iya haifar da ambaliyar ruwa a wurare 76 da ke jihohi 19 a Najeriya.
Cibiyar Gargadi kan Ambaliya ta Kasa da ke Ma’aikatar Muhalli ta kasa ce ya yi gargadin ranar Talata, inda ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da ma sauran jama’a da su dauki mataki.
Gargadin na zuwa ne ’yan kwanaki bayan samun wata mummunar ambaliyar a jihohin Legas da Filato da Anambra da Delta.
Kwamishina ya yi murabus kan ƙarbar belin dillalin ƙwayoyi a Kano Ruftawar gini ta kashe uwa da ’ya’yanta 5 a KatsinaAna has ashen samun mamakon ruwan saman ne daga daga biyar zuwa tar aga watan Agustan 2025.
Yankunan jihohin da za a iya samun ambaliyar a cewar cibiyar sun hada da Kano (Bebeji, Gezawa, Gwarzo, Birni da Kewaye, Karaye, Tundun-wada, Wudil, Kunchi); Kebbi (Bagudo, Birnin-Kebbi, Bunza, Gwandu, Jega, Kalgo, Kamba, Kangiwa, Shanga, Ribah, Sakaba, Saminaka, Yelwa, Gauri-Banza); Neja (Kontagora, Rijau, Ringim); Filato (Mangu); Taraba (Donga, Takum); Jigawa (Diginsa, Gumel, Dutse, Gwaram, Hadejia, Miga); Yobe (Machina, Potiskum); Zamfara (Anka); Sakkwato (Sakkwato, Wamakko); Borno (Biu); da kuma Gombe (Bajoga).
Sauran wuraren sun hada da Akwa-Ibom (Edor, Eket, Ikom, Oron, Upenekang); Bauchi (Tafawa-Balewa, Azare, Jama’are, Kari, Misau, Jama’a); Ebonyi (Abakaliki, Echara, Ezilo); Kuros Riba (Ogoja Edor, Obubra); Nasarawa (Keana, Keffi, Wamba); Binuwai (Agaku, Buruku, Gboko, Igumale, Ito, Katsina-Ala, Ugba, Vande-Ikya); Kaduna (Jaji, Kafancha, Birnin-Gwari, Zaria) sai kuma a jihar Katsina (Bindawa, Bakori, Daura, Funtua).
Ambaliyar ruwa dai ta zama wata babbar annoba da ke faruwa a Najeriya a kowacce shekara inda takan lalata dukiyoyin da ma rasa rayukwan jama’a.
Ko a bara, akalla jihohi 31 ne aka samu rahoton ambaliyar ruwa wacce ta kai ga rasa rayukan mutane da dama tare da shafar mutum miliyan daya da dubu 200.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliya
এছাড়াও পড়ুন:
Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet
Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa za a yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da tsawa na kwaki uku a faɗin ƙasar daga ranar Litinin.
NiMet ta fitar da wannan hasashen ne ranar Lahadi a Abuja, lamarin da ke ƙara barazanar ambaliya a wasu jihohin ƙasar.
Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura Najeriya na hasashen samun N300bn a shekara daga noman dabinoHasashen na zuwa ne bayan ruwan sama ya lalata gidaje kimanin 50 da gonaki da wuraren ibada a Jihar Filato.
Hukumar ta yi hasashen cewa za a yi tsawa da ruwan sama a jihohin arewacin ƙasar da suka haɗa da Adamawa da Taraba da Sakkwato da Kebbi da Zamfara da Jigawa da Kano da kuma Katsina ranar Litinin, kuma lamarin zai yi ƙamari zuwa yammacin ranar.
“Akwai yiwuwar samun ambaliya a wasu sassan jihohin Adamawa da Taraba da kuma Bauchi a wannan lokacin da aka yi hasashen,” kamar yadda NiMet ta bayyana a sanarwar.
A tsakiyar Nijeriya, ana sa ran saukar ruwan sama kaɗan da safiya a jihohin Binuwai da Neja da Kogi da Nasarawa da Kuma Birnin Tarayya Abuja.
Kuma zuwa rana da yamma, ana sa ran ruwan saman zai kai jihohin Filato da Kwara da kuma sauran jihohi maƙwabta.
A yawancin jihohin kudancin ƙasar dai hasashen hadari ake yi, inda ake ganin yiwuwar samun ruwan sama kaɗan a jihohin Ebonyi da Enugu da Imo da Anambra da Abia da Ogun da Edo da Delta da Legos da Ribas da Cross Rivers da Akwa Ibom da kuma Bayelsa da sanyina safiya.
Amma daga baya ana sa rai za a yi ruwa mai yawa, inda NiMet ke gargaɗin cewa za a iya samun ambaliya a jihohin Oyo da Ogun da Edo da kuma Delta.
Ranar Talata, hukumar tana hasashen cewa za a ci gaba da samun ruwan sama mai yawa da tsawa a yankin arewacin ƙasar musamman a jihohin Taraba da Katsina da Kebbi da Sokoto da Kaduna da kuma Zamfara.
“Ana tsammanin matsakaicin ruwan sama da tsawa a faɗin yankin daga baya a ranar,” in ji hukumar.
Jihohin tsakiyar ƙasar ciki har da Abuja, na tsammanin ruwan sama mai ɗaukewa da dawowa, yayin da jihohin kudancin ƙasar daga Legas zuwa birnin Calabar za su iya fuskantar ruwan sama babu ƙaƙƙautawa.
NiMet ta ja hankalin mazauna jihohin Anambra da Delta da Bayelsa da Cross River da kuma Akwa Ibom su shirya wa yiwuwar ambaliya.
Zuwa ranar Laraba, ana sa ran ruwan sama da tsawa zai karaɗe jihohin Taraba da Kaduna cikin sanyin safiya, inda kuma za a samu guguwa da ruwan sama daga baya a jihohin Borno da Bauchi da Gombe da Jigawa da kuma Kano.
Yankin tsakiyar ƙasar kuma zai sake ganin yayyafi da safiya, kuma da rana za a yi ruwan sama mai yawa.
A kudanci kuwa, ana hasashen za a yi ruwan sama mai ɗaukewa da dawowa a jihohin Legas da Ribas da Bayelsa da Cross River. Jihar Bayelsa ta fi fuskantar barazanar ambaliya a tsakiyar mako, in ji hukumar
Hukumar ta yi kira ga mazauna jihohin su ɗauki matakan kauce wa barazanar ambaliyar.
“[Ku] kaurace wa tuƙi a cikin ruwan sama mai ƙarfi, kuma jihohin da ke da yiwuwar samun ambaliya su yi tsare-tsarensu na ba da agajin gaggawa nan-take,” in ji hasashen.
NiMet ta kuma shawarci magidanta su ɗaure ababen da ka iya faɗuwa kuma su sanya rigunan sanyi tare da cire kayan laturoni daga lantarki a lokacin guguwa.
Hukumar ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama su nemi shawarwari na yanayi wajen shirya jadawalin jigilar matafiyansu.
NiMet ta buƙaci ‘yan Nijeriya su bibiyi shafinta na intanet don samun ƙarin bayani kan yanayi.