Aminiya:
2025-11-05@05:24:43 GMT

Ambaliya ta lalata kauyuka 3 a Sakkwato

Published: 6th, August 2025 GMT

Akalla magidanta 50 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kauyuka uku na karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato, sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka a yankunan.

Ambaliyar da ta mamaye kauyukan na Tangaza ne da suka hada da Gidan Madi da Baidi da Madarare, kuma ta haifar da rushewar gidaje da lalacewar gonaki da rijiyoyi da sauran su.

Yadda ’yan bindiga suka sace Zamfarawa 150 a cikin kwana 4 Duk wanda ya haka rijiyar burtsatse a Lekki ruwan masai yake sha – Gwamnatin Legas

Mutanen da lamarin ya shafa sun ce suna bukatar agajin gaggawa na abinci da magani da tsaftataccen ruwan sha.

Shugaban karamar hukumar ta Tangaza, Isah Salihu Kalenjeni, ya jagoranci wata tawaga sun ziyarci wuraren da lamarin ya shafa don ganin barnar da ambakiyar ta yi tare da jajanta wa mutanen yankunan.

A yayin ziyarar, Shugaban karamar hukumar ya tabbatar wa mutanen zai sanar da duk wata hukuma da ta dace don kawo masu daukin gaggawa kan halin da suke ciki.

Hukumomi a karamar hukuma da masu bayar da agajin gaggawa sun kuma yi kira wadanda iftila’in ya shafa da su yi aiki tukuru don kare barkewar annobar ciwo ga sauran al’umma.

Aliyu Na Abba daya daga cikin mutanen da ambaliyar ta rusa wa gida da gonaki biyu ya ce yana bukatar hukuma ta tausaya masa halin damuwar da shi da iyalansa suka fada.

Umaima Dan Umaru da ta ke da marayu uku a tare da ita ta ce gonakinsu biyu da suka yi shuka sun lalace sabadiyyar ambaliyar, don haka suna neman agaji.

Ta ce akalla akwai kusan mutum 50 da suka tafka asara a yankin nasu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ambaliyar ruwa Sakkwato

এছাড়াও পড়ুন:

Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar

Daga Usman Mohammed Zaria

Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Injiniya (Dr.) Muhammad Uba, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa amincewa da sabbin ayyukan gina hanyoyi a fadin jihar, ciki har da na Birnin Kudu.

Ya ce wannan mataki na cikin ajandar gwamnati 12, musamman wajen inganta ci gaban ababen more rayuwa.

A cewarsa, Birnin Kudu za ta amfana da gina hanyoyi masu tsawon kilomita 113, wanda ya hada da hanyoyin kauyuka da wadanda ke hada al’umma da sauran sassan jihar.

Dr. Uba ya bayyana aikin a matsayin babban ci gaba wajen saukaka zirga-zirga, inganta harkokin tattalin arziki da samun sauki ga muhimman ayyuka ga jama’a.

Ya bayyana tabbacin cewa za a dade ana cin moriyar aikin hanyoyin,  tare da hanzar ayyukan ci gaba da bunkasar karamar hukumar.

Shugaban ya yi addu’ar dorewar zaman lafiya da cigaba a Birnin Kudu tare da yin alkawarin ci gaba da hada kai da gwamnatin jiha domin tabbatar da cewa jama’a suna amfana da fa’idodin dimokuraɗiyya.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zargin Kisan Kiyashi Ga Kiristoci: Trump Bai San Ƙalubalen Tsaron Da Najeriya Ke Ciki Ba — Ndume
  • Ana Tattara Gawawwakin Mutanen Da Mayakan Rapid Support Forces Suka Kashe A Arewacin Kordofan Na Sudan
  • Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike
  • Uba Sani Ya Kaddamar Da Gidaje 100 Ga Waɗanda Rikici Ya Shafa A Jihar
  • Uwargidan Gwamnan  Zamfara Ta Yaba Wa  Karamar Hukumar Gusau Bisa Shirin Tallafawa Jama’a
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar
  • Yadda matata ta ɓace a Abuja aka tsince ta a Sakkwato
  • Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher
  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano