An shafe wata 8 ana mulki babu mataimakin gwamna a Tataba
Published: 7th, August 2025 GMT
Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya yi ɓatan dabo inda ya shafe tsawon watanni takwas ba tare da an gan shi ba.
Alkali, na fama da rashin lafiya tun a bara wanda hakan ya sa bai sake bayyana a bainar jama’a ba.
Majalisa ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a Bauchi Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arzikiAn fara kula da lafiyarsa a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, daga baya aka kai shi ƙasar Masar domin ci gaba da jinya.
Gwamna Agbu Kefas, ya naɗa Emmanuel Lawson, ɗaya daga cikin mataimakansa, domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan ofishin mataimakin gwamnan.
A wata wasiƙa da Sakataren Gwamnatin Jiha ya sanya wa hannu, an ce naɗin zai taimaka wajen tabbatar da ingantaccen shugabanci.
Sai dai wasu na ganin Lawson bai cancanci riƙe wannan ofishi ba saboda ba zaɓar shi aka yi ba.
Gwamnati ta ce yana murmurewaGwamnatin jihar ta bayyana cewa Alhaji Aminu Alkali na murmurewa daga ciwon shanyewar ɓarin jiki da ya shafi lafiyarsa da yanayin maganarsa.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Bordiya Buma, ya kai masa ziyara a watan Maris kuma ya ce yana samun sauƙi.
“Muna farin ciki da samun sauƙi da yake yi kuma muna fatan zai dawo nan ba da jimawa ba.”
Sai dai har yanzu bai dawo bakin aiki ba.
Wasu rahotanni na cewa yana Abuja yana ci gaba da jinya, wasu kuma na cewa yana zaune a wani gida a unguwar Wuse.
A gefe guda kuma, ma’aikatansa sun ce ba sa ganinsa ba.
’Yan adawa na neman ba’asiWasu ‘yan siyasa da jama’a suna buƙatar gwamnati ta bayyana gaskiyar halin da mataimakin gwamnan jihar ke ciki.
“Mutanen Taraba suna da ‘yancin sanin inda mataimakin gwamna yake da halin da lafiyarsa ke ciki,” in ji Alhaji Hassan Jika Ardo, tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar.
Ya ce gwamnati ta daina wasa da hankalin jama’a a kan batun da dokar ƙasa ta bayyana a fili.
Dalilin da ya sa ba a sauke shi baSashe na 189 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bayyana cewa za a iya tsige mataimakin gwamna ne kawai idan kwamitin likitoci ya tabbatar cewa ba shi da ƙoshin lafiyar da zai iya kataɓus.
Wannan na buƙatar ƙuri’a daga kashi biyu bisa uku na majalisar zartarwa ta jihar.
Har yanzu ba a ɗauki wannan matakin ba.
Siyasa ta hana a ɗauki matakiWasu majiyoyi sun ce ana matsa wa gwamnan jihar lamba kan ya sauke mataimakin nasa, amma yana tsoron kada hakan ya rushe tsarin rabon madafun iko tsakanin yankunan jihar.
Sauya mataimakin gwamnan na iya janyo rikicin siyasa a jihar.
An taɓa fuskantar irin wannan rikici a TarabaA shekarar 2012, Gwamna Danbaba Suntai, ya yi hatsarin jirgin sama kuma bai samu sauƙi ba na tsawon watanni.
Rikici ya ɓarke saboda ba a bayyana halin da yake ciki ba, kuma bai miƙa wa majalisa wasiƙar cewa ba zai iya ci gaba da aiki ba.
Wannan ya janyo rikici da rarrabuwar kawuna tsakanin masu goyon bayan gwamnan da na mataimakinsa.
Ra’ayoyin lauyoyi sun bambantaWasu lauyoyi sun ce lokaci ya yi da gwamnati za ta aiwatar da dokar ƙasa.
“Rashin lafiyar mataimakin gwamna ta shafi ci gaban jihar. Idan ba zai iya aiki ba, ya kamata ya sauka,” in ji lauya mai kare haƙƙin bil’adama, Malachy Ugwumadu.
Amma wani babban lauya, Richard Ahonaruogho (SAN), ya ce jihar ba ta cikin matsala dangane da rashin lafiyarsa.
“Muddin gwamna bai koka cewa ba zai iya aiki ba, babu buƙatar ɗaukar mataki,” in ji shi.
Jama’a sun fara gajiyaYayin da aka shafe tsawon lokaci babu mataimakin gwamnan, mutane da dama a jihar suna fara nuna damuwa.
Wasu na ganin rashin bayyana gaskiya yana nuna rashin girmama masu kaɗa ƙuri’a.
Yanzu dai idanun mutane sun karkata ne kan gwamnan da majalisar dokokin jihar domin su bayyana gaskiya ko su ɗauki matakin doka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: mataimakin gwamna Rashin lafiya Siyasa Taraba mataimakin gwamnan mataimakin gwamna
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140
“Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na musamman. Ya ce hakan zai rage cunkoso, ya haɗa al’umma, ya kuma farfaɗo da kasuwancin ƙauye da birane.
A fannin lafiya, gwamnati ta ƙaddamar da gina sabon babban asibiti a Nasarawa Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, tare da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya da dama a yankunan karkara, domin sauƙaƙa samun ingantaccen magani.
An kuma sanar da ci gaba da gyaran makarantu a dukkan ƙananan hukumomi, tare da samar da kujeru, littattafai, kayan koyo da horar da malamai domin tabbatar da ingantaccen ilimi ga yaran jihar.
Haka kuma, ana gina sabuwar kasuwa ta zamani a Nasarawa Burkullu, da ake sa ran za ta zama cibiyar bunƙasa sana’o’i da kasuwanci ga mazauna yankin. A bangaren ruwa da wutar lantarki kuwa, ana tono ruwan sha da kuma shimfiɗa sabbin hanyoyin rarraba wuta zuwa asibitoci, makarantun firamare da sakandare, da cibiyoyin gwamnati.
Dantawasa ya ce, an riga an kammala wasu daga ayyukan tare da ƙaddamar da su, yayin da sauran ke kan gaba, abin da ya tabbatar da cewa gwamnatin Lawal “ba ta tsaya kan magana kawai ba, tana aiki tare da sakamako a fili wanda jama’a ke iya gani da idonsu.”
“Wannan gwamnati ta tsayu kan gaskiya, amana, da samar da kyakkyawan sakamako ga al’umma. Ayyukan da ake gani su ne shaida,” inji Kwamishinan.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA