Kamaru: An haramta wa abokin hamayyar shugaban kasar tsayawa takara a zaben Oktoba
Published: 6th, August 2025 GMT
Majalisar tsarin mulkin kasar Kamaru ta amince da matakin haramta wa babban abokin hamayyar shugaba Paul Biya Maurice Kamto tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 12 ga watan Oktoba.
A watan Yulin da ya gabata ne dai hukumar zabe ta fitar da Kamto daga jerin sunayen ‘yan takarar da aka amince da su.
Kamto ya daukaka kara a cikin kwanaki biyu. Sai dai shugaban majalisar tsarin mulkin kasar, Clement Atangana, ya amince da hukuncin haramta masa tsayawa takarar. Ba a iya samun damar jin ta bakin Kamto ba don yin tsokaci, a cewar Reuters.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce matakin da hukumar zaben kasar Kamaru ta dauka na haramta wa Kamto tsayawa takara ya haifar da damuwa game da sahihancin tsarin zaben kasar.
Dubban masu zanga-zanga ne suka taru a kofar Majalisar Tsarin Mulki a ranar Litinin domin nuna goyon bayansu ga Kamto, amma ‘yan sanda sun tarwatsa su da hayaki mai sa hawaye.
Kwamishinan ‘yan sandan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “an kama mutane da dama kuma suna ci gaba da tsare su domin gudanar da bincike.
A zaben da ya gabata a shekarar 2018, Kamto ya zo na biyu da kashi 14% na kuri’un da aka kada, yayin da Biya ya samu gagarumin rinjaye, wanda ‘yan hamayya da ma wasu bangarori na kasa da kasa ke ganin cewa an tabka magudia zaben.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Yunkurin Netanyahu na mamaye Gaza ya tayar da balli a Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 6, 2025 Araqch: Hadin Kai Tsakanin Cibiyoyi Na Tabbatar Da Karfi Da Ci Gaba August 5, 2025 Wilayati: Iran Ba Za Ta Amince Da Yin Amfani Da Hanyar Zangezur Ta Hanyar Da Bata Dace Ba August 5, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Da Ke Yankin Jaffa Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 5, 2025 Dr Muhammad Tahir Da Aka Yi Wa Barazanar Kisa Ya Bayyana Abin Da Ya Gani Na Masifa A Gaza August 5, 2025 An Samu Bullar Sabani Da Rikici Tsakanin ‘Yan Sahayoniyya Game Da Batun Mamaye Zirin Gaza August 5, 2025 Jiniyoyin Gargadi Sun Tashi A HKI Bayan Da Yemen Ta Cilla Sabbin Makamai August 5, 2025 Iran Ta Kafa Kwamitin Tsaron Kasa Wanda Zai Kula Da Sabbin Matsalolin Tsaro August 5, 2025 Rasha Zata Kara Kyautata Dangantaka BRICS don Magance Takunkuman Amurka A Kanta August 5, 2025 Gagarumar Zanga-Zang A birnin Paris Na kasar Faransa Saboda Killace Gaza August 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin HKI A Kudancin Lebanon
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta sanar a yau Litinin cewa; Jirgin sama maras matuki na HKI ta kai wa wata mota hari a kusa da garin “Sharqiyya”.
Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon kuwa ya sanar da cewa; Jirgin sama maras matuki na HKI ya jefa bom a kusa da wata motar Buldoza a garin Khayyam, sai dai babu wanda ya jikkata.
Haka nan kuma kamfanin dillancin labarun ya ce; Jirgin saman maras matuki ya jefa wasu bama-baman guda uku akan hanyar Zafta.
A cikin kwanakin bayan na HKI tana kara tsananta kai hare-hare a kudancin Lebanon, lamarin da yake nuni da kokarin sake dawowar yaki gadan-daban.
Tun bayan tsagaita wutar yaki a Lebanon shekarar da ta gabata HKI take keta hurumin kasar ta Lebanon ba tare da kakkautawa ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha November 3, 2025 An Sami Tsaikon Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Tanzania Saboda Rikicin Zabe November 3, 2025 Falasdinawa Biyu Sun Yi Shahada A Nablus Da Khalil November 3, 2025 Jagora: Sabanin Jamhuriyar Musulunci Da Amurka Daga Tushen Manufa Ne Ba Sama-sama Ba November 3, 2025 Turkiyye na karbar taron Kasashen Musulmi Kan Halin Da Ake Ciki A Gaza November 3, 2025 Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan tsagaita wuta a Gaza November 3, 2025 Girgizar kasa ta yi ajalin gomman mutane a Afghanistan November 3, 2025 Najeriya : tun kafin kalamman Trump muka dauki matakai November 3, 2025 Sudan : Mutane 1,500 sun rasa matsugunansu sakamakon tashin hankali November 3, 2025 UNICEF Tayi Gargadi Game Da Mawuyacin Hali Da Yara Ke Ciki A Gaza November 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci