Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a Neja
Published: 6th, August 2025 GMT
Mutum 22 sun gamu da ajalinsu, yayin da wasu 20 suka jikkata, bayan wata babbar mota da ta yi lodin mutane da dabbobi ta yi hatsari a kan hanyar Lambata zuwa Lapai da ke Jihar Neja.
Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Litinin.
Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murna Ambaliya ta lalata kauyuka 3 a SakkwatoMotar ta taso daga Kano zuwa Legas ne lokacin da hatarin ya auku da misalin ƙarfe 3 na safe, sakamakon gudun wuce ƙima.
Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta ce dukkanin fasinjojin da ke cikin motar maza ne.
An kai gawarwakin Babban Asibitin Suleja, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati na Lambata.
Daga baya, iyalan wasu daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su, sun ɗauke su zuwa wasu cibiyoyin lafiya.
Jama’a sun ce hatsarin mota na ci gaba da zama ruwan dare a hanyar Lambata zuwa Bida, musamman manyan motocin dakon kaya da ke ɗauko mutane da dabbobi a lokaci guda.
Wasu sun ɗora laifi kan lalacewar hanya, gudun wuce ƙima da rashin bin dokokin hanya.
Aƙalla mutum 80 ne suka rasu a wannan hanya cikin shekarar da ta gabata.
Wasu mazauna yankin sun ce hanyar tana hatsari sosai ga ƙananan motoci da masu babura, saboda yawan manyan motoci da ke zirga-zirga a hanyar.
Sun buƙaci gwamnati da ta gyara hanyar, tare da ɗaukar mataki kan direbobi masu ganganci.
Ana ci gaba da aikin gyaran hanyar Lambata-Lapai-Agaie-Bida ƙarƙashin wani shiri na NNPC.
Amma sai an kammala aikin da kuma kafa dokoki masu tsauri kan zirga-zirgar ababen hawa, jama’a na fargabar cewa za a iya ci gaba da salwantar rayuka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hatsarin mota Manyan motoci hanyar Lambata
এছাড়াও পড়ুন:
An sace jariri sabuwar haihuwa a asibitin Ekiti
An nemi wani jariri sabuwar haihuwa an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin.
Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririn ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarsa da safiyar wannan Litinin ɗin.
Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙuraLamarin na ba-zato-ba-tsammani ya haifar da fargaba musamman yadda ɗimauta uwar jaririn da kuma wasu daga cikin mutanen da ke cikin harabar asibitin.
Tuni dai an garzaya da ma’aikatan da ke kula da ɗakin haihuwa da uwar jaririn da mai gadi da wasu da ake zargi zuwa ofishin ’yan sanda domin ci gaba da bincike.
Aminiya ta ruwaito cewa wasu masu neman na abinci a kusa da asibitin sun shiga ɗimuwa matuƙa dangane da faruwar lamarin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda na jihar, SP Sunday Abutu, ya ce yanzu haka akwai mutum huɗu da ake zargi da suka shiga hannu, “kuma suna bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka a binciken.”
Abutu ya ce Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Joseph Eribo, ya umurci sashen bincike na musamman (CID) da su gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da dawo da jaririn cikin ƙoshin lafiya.