Jihar Zamfara: ‘Yan Sanda 390 Sun Sami Karin Girma
Published: 6th, August 2025 GMT
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya kawata jami’ai 390 da aka daga matsayinsu zuwa sabon mukami a rundunar.
An gudanar da bikin kawata jami’an ne a Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda da ke Gusau, babban birnin jihar.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sanda, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, Kwamishinan ‘Yan Sanda ya taya sabbin jami’an murna tare da bukatar su tabbatar da cancantarsu da mukaman da aka ba su, ta hanyar rubanya kishin aiki, ladabi da kwarewa a ayyukansu.
Ya jaddada bukatar jami’an da su dage wajen yin aiki da jajircewa da kuma bayar da ingantaccen tsaro ga al’ummar Jihar Zamfara da Najeriya gaba ɗaya.
Daga cikin waɗanda suka sami karin girman akwai CSP Sani Kabiru da CSP Usman M. Nassarawa, waɗanda aka daga zuwa mukamin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda (ACP).
“An daga jami’ai 30 daga matsayin Sifeto zuwa Mataimakin Sufiritandan ‘Yan Sanda (ASP II).” In ji Kwamishinan.
Ya ƙara da cewa, an daga jami’ai 242 daga Sajan zuwa Sufeta, sannan kuma an daga jami’ai 116 daga matsayin Kofur zuwa Sajan.
Da yake magana a madadin sabbin jami’an da aka daga matsayinsu, ACP Usman M. Nassarawa ya nuna godiya sosai ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda bisa amincewar da suka nuna a gare su.
Ya yi alkawarin cewa sabbin jami’an za su ci gaba da kiyaye manyan dabi’un aikin ‘yan sanda na Najeriya – wato gaskiya, jajircewa, ƙwarewa da amincewar jama’a – a hidimarsu ga ƙasa.
Daga Aminu Dalhatu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba
A halin yanzu, sashen saukar kumbuna da dukkan na’urori da tsare-tsaren da ke aikin tallafa wa saukar kumbo suna ci gaba da shirye-shiryen tarbar ‘yan sama jannatin, kamar yadda Hukumar Kula da Zirga-zirgar Kumbuna ta kasar Sin ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA