Majalisa ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a Bauchi
Published: 7th, August 2025 GMT
Majalisar Dokokin Bauchi ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a fadin jihar domin haɓaka ci gaba, inganta shugabanci, da kawo sauƙin gudanar da mulki.
Wannan na ƙunshe ne a wani ƙudiri da dan majalisar mai wakiltar mazabar Disina, Sale Hodi Jibir, ya gabatar a yayin zaman da Kakakin Majalisar, Abubakar Y.
A cewar Jibir, ƙudurin yana dogaro ne da tanadin kundin tsarin mulki na 1999 wanda ya bai wa majalisun dokokin jihohi damar fara shirin ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi, matuƙar an cika wasu sharuɗa da suka haɗa da goyon bayan kashi biyu bisa uku na mambobin majalisa, da mincewar ƙananan hukumomin da abin ya shafa da kuma gudanar da zaɓen raba gardama.
Jibir ya bayyana cewa ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi zai sauƙaƙa rarraba albarkatu cikin adalci da inganta shugabanci da gudanarwa a matakin ƙasa da ƙarfafa haɗin kan al’umma da ci gaban tattalin arziki.
Ya kuma ce yankuna da dama a Jihar Bauchi sun gabatar da buƙatar a ware musu ƙaramar hukuma, musamman duba da girman yankunansu, yawan al’umma, bambancin al’adu da kuma ƙalubalen gudanar da mulki.
Jibir ya buƙaci a kafa kwamitin wucin gadi na musamman domin tattarawa da tantance buƙatun al’umma, da tuntuɓar sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da nazarce-nazarce kan fadin ƙasa, da yawan jama’a da yanayin tattalin arziki na yankunan da ake neman a samar musu da ƙananan hukumomi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ƙudirin wanda ya samu goyon bayan wasu mambobin majalisar da suka buƙaci a gaggauta aiwatar da shi domin amfanin jama’a sun haɗa da Jamilu Umaru Dahiru da Musa Wakili Nakwada da Ibrahim Tanko Burra da Sa’idu Sulaiman Darazo da Dokta Nasiru Ahmed Ala.
A wani ɓangare na zaman, majalisar ta amince da rahoton kwamitinta na ma’aikata, dangane da ƙorafe-ƙorafen rashin biyan ’yan fansho da albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi a faɗin jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Bauchi Ƙananan Hukumomi Majalisar Dokokin Bauchi ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi
এছাড়াও পড়ুন:
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Li Chenggang, wakilin cinikayyar kasa da kasa na ma’aikatar kasuwanci kuma mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin, ya gana da tawagar cinikayyar kayan noma ta Amurka a birnin Beijing a jiya Talata 4 ga watan Nuwamb, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi kan huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, da cinikayyar kayayyakin noma, da sauran batutuwa masu alaka.
Li Chenggang ya bayyana cewa kyakkyawar alaka ta tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka tana da alfanu ga kasashen biyu da kuma duniya baki daya. Tun daga watan Mayu na wannan shekarar, tawagogin tattalin arziki da cinikayya na bangarorin biyu sun tattauna har sau biyar bisa jagorancin muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, wanda hakan ya karfafa daidaituwar alakar tattalin arziki da cinikayyar Sin da Amurka. Wannan ya tabbatar da cewa, Sin da Amurka suna da yakini a kan ci gaba da samun daidaito, girmamawa, da kuma cin gajiyar juna, kuma za su iya samun mafita a kan matsaloli ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa.
A nasu bangaren, membobin tawagar ta Amurka sun bayyana cewa kasar Sin muhimmiyar kasuwa ce ta fitar da kayan noma na Amurka, kuma manoman Amurka suna girmama hadin gwiwar da ke tsakaninsu da kasar Sin, kana suna da niyyar hada hannu don fadada hadin gwiwa da kasar Sin. Sun kara da cewa, dangantakar tattalin arziki da cinikayya mai dorewa tsakanin kasar Sin da Amurka tana da matukar muhimmanci ga cinikin kayan noma tsakanin kasashen biyu, kuma suna fatan ci gaba da samun kyakkyawan yanayin bunkasa huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA