Tinubu Ya Umurci A Bada Kulawar Lafiya Kyauta Ga Tsofaffin Ma’aikata Masu Karamin Fansho
Published: 6th, August 2025 GMT
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta aiwatar da shirin bayar da kulawar lafiya kyauta ga tsofaffin ma’aikata masu ƙaramin albashi da ke ƙarƙashin tsarin fansho na haɗin gwiwa (Contributory Pension Scheme – CPS), yana mai bayyana shirin a matsayin muhimmin bangare da zai taimaka wa rayuwarsu.
A wata sanarwa da mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma bada umarnin a gaggauta aiwatar da karin fansho da aka dade ana jiran shi, tare da kafa mafi ƙarancin adadin fansho domin kyautatawa tsofaffin ma’aikata mafi rauni a tsarin CPS.
Wannan umarni ya biyo bayan bayani da Daraktar Janar ta Hukumar Kula da Fansho ta Ƙasa (PenCom), Ms. Omolola Oloworaran, ta gabatar wa Shugaban ƙasa.
Shugaba Tinubu ya kuma umurci Daraktar Janar ta PenCom din da ta gaggauta warware matsalar fanshon ’yan sanda da ta daɗe tana ci gaba, yana mai jaddada cewa ’yan sanda samar da tsaro a ƙasa suna da hakkin samun fansho cikin mutuntawa da kwanciyar hankali.
Daraktar Janar din ta kuma sanar da Shugaban ƙasa yadda ake ƙoƙarin kare darajar asusun fansho duba da hauhawar farashi da matsin tattalin arziki, da kuma shirin kaddamar da tsarin ba da gudummawar fansho da kudin waje domin bai wa ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje damar shiga tsarin fansho.
Shugaba Tinubu ya nuna cikakken goyon bayansa ga waɗannan gyare-gyare, yana mai sake jaddada aniyar gwamnatinsa na bunƙasa ci gaba mai ɗorewa da kare rayuwar talakawan Najeriya.
Daga Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Neja Ya Bada Umarnin Sake Bude Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, Lapai.
Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya bayar da umarnin bude jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai domin fara gudanar da karatu na yau da kullun.
Umurnin sake bude jami’ar ya biyo bayan nazari sosai kan matakan tsaro da inganta ababen more rayuwa a jami’ar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Neja Alhaji Abubakar Usman ya rabawa manema labarai ta hannun jami’in yada labaran sa Lawal Tanko a Minna.
Ya ce Gwamna Bago ya gamsu da ingantaccen gine-ginen tsaro da ci gaban ababen more rayuwa da aka yi don kare dalibai da ma’aikata da kuma al’ummar Jami’ar.
Sakataren Gwamnan Jihar Neja dai ya jaddada jajircewar Gwamnati wajen kare jin dadin dalibai da ma’aikata tare da tabbatar da ci gaban ilimi ba tare da katsewa ba.
Alhaji Abubakar Usman ya yaba da kokarin hadin gwiwa da jami’an tsaro da hukumomin jami’ar da shugabannin al’umma ke yi wajen magance kalubalen da ya kai ga rufe jami’ar.
A cewarsa, “Gwamna Bago, yayin da yake amincewa da sake bude taron, ya jaddada cewa, tsaro da jin dadin dalibai da ma’aikata su ne babban fifiko ga gwamnatinsa, ya kuma jaddada kudirinsa na inganta ilimi a matsayin ginshikin ci gaba, tare da tabbatar wa al’ummar Jami’ar goyon bayan gwamnati”.
Sanarwar ta yi kira ga daukacin dalibai da ma’aikatan da suka dawo da su bi ka’idojin tsaro da kuma bayar da cikakken hadin kai ga mahukuntan Jami’ar domin a sami zaman lafiya.
An rufe jami’ar na wani dan lokaci ne saboda matsalar tsaro da kuma asarar rayuka da aka yi a tsakanin al’ummar jami’ar, wanda a yanzu ake sa ran za a ci gaba da aiki a yau Litinin 4 ga watan Agusta ashirin da biyar.
ALIYU LAWAL