Majalisar Katsina ta amince da sabuwar Dokar Masarautu
Published: 5th, August 2025 GMT
Majalisar Dokki ta Jihar Katsina ta amince da sabuwar Dokar Masarautu ta jihar, bayan ta yi wa daftarin dokar karatu na daya har zuwa na uku.
A sabuwar dokar da aka yi wa kwaskwarima, wadda take jiran sa hannun Gwamna Umaru Dikko Radda, gwamnan jihar ne kadai ke da ikon daga darajar sarki.
Kazalika ta ba wa gwamnan jihar kadai ikon zabar masu zabar sarki, sa’annan ta kara yawan da masu zaben sarki daga mutane hudu zuwa biyar.
Kauran Katsina, Galadiman Katsina, ’Yandakan Katsina da Durbi su ne mutum hudu da aka sani a mastayin masu zabar sarki, amma yanzu dokar ta da Marusan Katsina Hakimin Shargalle, sarautar da aka ba wa tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika.
Gobara ta cinye gidan hakimi a Bauchi Nafisa ta cancaci kyautar Dala 100,000 da gida da OON —Pantami Ɗaliba ’yar shekara 15 daga Yobe ta lashe Gasar Muhawara ta DuniyaA makon da ya gabata ne masarautar ta ba wa Hadi Siriki wannan sarauta wadda aka dauke ta daga Dutsi, yayin da ita Dutsin kuma aka mayar da Baburtau a matsayin mukamin Hakimin.
Gabanin wannan sabuwar doka a satin da ya gabata ne Masarautar Katsina ta fitar da sunayen wasu hakiman da aka kirkiro a masarautar.
Bayan waccan sanarwa, sai kuma ga kwafin ita wannan doka wadda majalisar ta yi wa karatu na yawo a kafofin sada zumunta.
Kazalika, akwai ’yan Majalisar Masarautun na Katsina da Daura wadanda aka yi wasu canje-canje.
A yanzu ’yan majalisar sun qunshi wakilai biyu da malamai, biyu daga attajiran jihar, wakili daga sashen kungiyoyin matasa. Sauran su ne, wakilin Kwamishinan Kananan Hukumomi, wakili daga Ma’aikatar Masarautu da masu zaben sarki.
Hatta da Sakataren Majalisa za a turo shi ne daga gwamnati maimakon a da sarki ne ke zabar shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: dokar masarautu Masarautar Katsina masu zabar sarki Sabuwar Doka
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi da ta karfafa matakan yiwa kananan hukumomin jihar 27 jagoranci akan sha’anin mulki da harkokin kudi domin inganta ayyukan su.
Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki 3 da kwamatin ya yi a ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar a Dutse.
Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa a majalisar dokokin jihar Jigawa, ya ce ziyarar kwamatin na da nufin tantance yadda ma’aikatar ta ke gudanar da ayyukan ta, ta fuskar harkokin mulki da na kudi da kuma dangantakar aiki tsakanin ta da kananan hukumomin jihar 27 kamar yadda tsarin mulki ya dorawa majalisa nauyi.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban Kwamatin kuma wakilin mazabar Kaugama, Alhaji Sani Sale Zaburan ya bayyana bukatar ganin jami’an ma’aikatar da ke kula da kananan hukumomi a shiyya shiyya suna gudanar da ayyukan su ba tare da jingina da shugabannin kananan hukumomi ba a ko da yaushe amma Kuma su na yiwa kananan hukumomin jagoranci wajen gudanar da sha’anin mulki da harkokin Kudi kamar yadda ya kamata.
Daya daga cikin ‘yan kwamatin Malam Ibrahim Sabo Ahmad Roni ya duba kundin bayanan sha’anin mulki yayin da Oditoci su ka duba kundin bayanan harkokin Kudi tare da yabawa da kuma bada shawarwari da za su inganta ayyukan ma’aikatar.
Da ya ke mayar da jawabi, kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi Alhaji Ibrahim Garba Hannun Giwa wanda Babban Sakatare na maikatar ya wakilce shi, Alhaji Muhammad Yusha’u ya ce ma’aikatar ce ke uwa da makarbiya wajen yiwa kananan hukumomi jagoranci a sha’anin mulki da harkokin Kudi da zamantakewa domin kawo cigaba a yankunan karkara.
Kazalika, a daya bangaren kuma, karamin Kwamatin da Babban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa ya kafa bisa jagorancin wakilin mazabar Kiyawa Alhaji Yahaya Muhammad Andaza domin duba aikin gyaran gidajen kananan hukumomin jihar 27 da ke kan titin Bypass a Dutse ya mika rahoton sa ga babban kwamatin.
Alhaji Yahaya Muhammad Andaza Wanda sakataren Kwamatin Alhaji Yusha’u Muhammad ya wakilta, ya ce karamin Kwamatin ya duba gidajen Inda ya dauki samfur din yanayin da su ke ciki.
Ya ce daga cikin gidajen akwai wadda ke funskatar matsaloli kamar na tsagewar bango da sanya darduma da kujeru da kayan amfani a dakin girki marasa inganci yayin da ba a mayar da na’urar sanyaya daki a wasu gidajen ba.
Yusha’u wanda shi ne mataimakin Akawun majalisar, ya lura cewa akwai rashin kyawun flasta a wasu gidajen yayin da kan dakin wasu ke yayyo sai Kuma rashin fankar sama da karayyayun kujeru da rashin hada wasu gidajen da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da rashin kyawun kofofi da magudanin ruwa da ke kawo barazanar ambaliyar ruwa ga wasu gidajen.
A nasa jawabin, shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakari ya ja hankalin shugabannin kananan hukumomin jihar da su dauki nauyin cikakkiyar kulawa ga gidajen bisa la’akari da dinbin kudaden da aka kashe wajen gyara gidajen.
Usman Mohammed Zaria