Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC
Published: 7th, August 2025 GMT
Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci ta EFCC, Ola Olukoyede, ya ce galibin rukunin gidajen da aka fara amma aka yi watsi da su a Abuja na ma’aikatan gwamnati ne da suka mallaka da kudaden sata.
Ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Laraba yayin wata tattaunawa da wata kungiyar lauyoyi mai suna Law Corridor ta shirya mai taken “Manyan kalubalen da ke fuskantar sana’ar rukunin gidaje a Najeriya“.
Ya ce akwai irin wadannan gidajen da aka yi watsi da su sama da shekara 10, inda ya ce tuni hukumar ta kafa kwamiti na musamman da zai fara ziyartar irin gidajen.
Ola ya ce, “Na kafa kwamitin. Za mu fara ziyartar irin wadannan gidajen ba wai a iya Abuja ba, a duk fadin Najeriya. Muna so mu san mamallakansu.
“Abin da zai ba ka mamaki shi ne wasu daga cikin wadannan gidajen an yi watsi da su sama da shekaru 10 zuwa 20 ba tare da an waiwaye su ba. Kawai da zarar sun kai wani mataki sai a yi watsi da su.
“Babu wanda ya san me ke faruwa. Amma abin da muka iya ganowa shi ne yawancin irin wadannan rukunin gidajen na ma’aikatan gwamnati ne da suka saci kudade.
“Da zarar sun bar aiki sai kudaden su daina shigowa sai su dakatar da aikin. Shi kuma magini sai ya fara neman masu zuba jarin da zai taimaka musu su karasa aikin,“ in ji shi.
Shugaban na EFCC ya ce ko a ’yan kwanakin nan sai da hukumar ta kwace irin wadannan gidajen sama da 15.
“Muna da bayanan sirri. Wasu daga cikinku da ke zaune a nan ma watakila na cikin masu irin wadannan gidajen,“ in ji Shugaban na EFCC.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: irin wadannan gidajen yi watsi da su
এছাড়াও পড়ুন:
Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanata Barau Zai Yi Ƙarar Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10 November 8, 2025
Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025
Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025