Malaman Jami’o’in Isra’ila Sun Nemi Jamus Ta Tilasta Dakatar Da Yakin Gaza
Published: 6th, August 2025 GMT
Malaman jami’o’i sama da 100 daga Isra’ila sun bayyana cewar jan kafar da ƙasar Jamus ke yi wajen ɗaukar matakin matsin lamba ga gwamnatin Isra’ila na iya bai wa ƙasar damar ci gaba da aikata manyan laifuffuka a Gaza.
Wata wasika da masanan suka rubuta wa ɗaya daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar SPD da ke mulki a Jamus, ta ce rashin ɗaukar matakin na iya bada damar gudanar da wasu sabbin laifuffuka a Gaza, tare da watsi da irin tarihin da aka koya a shekarun baya.
A ranar 22 ga watan Yuli, biyu daga cikin jiga jigan kawancen jam’iyyun dake jagorancin Jamus, sun bukaci ƙasar da ta shiga cikin ƙasashen duniya da ke ƙawance domin gaggauta kawo ƙarshen yaƙin Gaza da kuma sanya takunkumi a kan Isra’ila da kuma kin sayar mata da makamai.
Gwamnatin Jamus da ke ƙarƙashin ƙawance jam’iyyun CDU da SCU da kuma SPD ta ƙarfafa sukar da take yiwa gwamnatin Isra’ila a kan yadda take azabtar da mazauna Gaza wajen hana kai musu kayan agaji, amma kuma ya zuwa yanzu bata bayyana ɗaukar wasu matakai masu tsauri ba.
Isra’ilar dai ta yi watsi da duk wani yunkuri na zargin da ake mata na amfani da yunwa wajen azabtar da mutane akalla miliyan biyu dake zama a Gaza, inda ta bayyana cewar ƙungiyar Hamas ce ke sace abincin da ake kai wa mutanen yankin.
Matakan kai hari a kan masu neman kayan agajin da Isra’ila ke yi a kan mazauna Gazar, sun yi sanadiyar hallaka akalla mutane sama da dubu guda.
Kungiyar Hamas ta ƙaddamar da harin da ya hallaka Yahudawa sama da 1,200 a watan Oktobar shekarar 2023, abinda ya sa Isra’ila ƙaddamar da yakin da ya hallaka mutane sama da 50,000 a bangaren Falasdinawa.
Tuni ƙasashen Birtaniya da Canada da kuma Faransa suka bayyana aniyarsu ta amincewa da ƙasar Falasdinu a taron Majalisar Ɗinkin Duniyar da zai gudana a watan Satumba, inda suke cewa ta wannan hanyar ce kawai za a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Isra’ila da Amurka sun bayyana matuƙar ɓacin ransu da matakin, yayin da a yau Firaminista Benjamin Netanyahu ke cewa ba zai dakatar da yakin da yake yi ba har sai ya murkushe ƙungiyar Hamas.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Iran: Yakin Kwanaki 12 Ya Bayyana Inganci Da Karfin Yakin Yanar Gizo Na Kasar
A dai dai lokacinda ake yaki na kwanaki 12 tsakanin Iran da HKI da Amurka, daga ranar 13-24 na watan Yunin da ya gabata, cibiyoyin yakin yanar gizo na kasar Iran sun gwada karfinsu da kuma kwarewansu a wannan fagen fama.
Kanfanin dillancin labarai na Tasnim na kuma kasar Iran ya nakalto sharhin wasu kafafen yada labarai na kasashen yamma dangane da shi.
Makarantar Midle East Institute ya dubi wannan al-amarin a cikin wabi bayani da ya fitar. Inda yake cewa cibiyoyin yakin yanar gizo na Iran sun shagaltu a wannan lokacin da kare cibiyoyin kasar Iran, amma ta kuma ya aiki da kare kasar taga makiya musamman masu taimakawa HKI a wannan yakin. Kuma da hakan ta kare wurare da dama a kasar, musamman hare-hare kan bankuna. Da ciboyoyin kudi don hargitsa su.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran: An nada Larijani a matsayin sakataren kwamitin koli na tsaron kasa August 6, 2025 Sheikh Qassem: Tsaron Isra’ila zai rushe cikin sa’a 1 idan ta shelanta yaki a kan Lebanon August 6, 2025 Kwamitin Sulhu na MDD ya yi zaman gaggawa kan batun Gaza August 6, 2025 Kamaru: An haramta wa babban dan hamayya tsayawa takara a zaben Oktoba August 6, 2025 Yunkurin Netanyahu na mamaye Gaza ya tayar da balli a Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 6, 2025 Araqch: Hadin Kai Tsakanin Cibiyoyi Na Tabbatar Da Karfi Da Ci Gaba August 5, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Da Ke Yankin Jaffa Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 5, 2025 Dr Muhammad Tahir Da Aka Yi Wa Barazanar Kisa Ya Bayyana Abin Da Ya Gani Na Masifa A Gaza August 5, 2025 An Samu Bullar Sabani Da Rikici Tsakanin ‘Yan Sahayoniyya Game Da Batun Mamaye Zirin Gaza August 5, 2025 Jiniyoyin Gargadi Sun Tashi A HKI Bayan Da Yemen Ta Cilla Sabbin Makamai August 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci