Iran: An nada Larijani a matsayin sakataren kwamitin koli na tsaron kasa
Published: 6th, August 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya nada Ali Larijani babban mai baiwa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara a matsayin sabon babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasar.
Larijani ya taba rike mukamin sakataren majalisar koli ta tsaron kasar daga ranar 15 ga watan Agustan shekarar 2005 zuwa ranar 20 ga watan Oktoban shekarar 2007, sannan ya rike mukamin kakakin majalisar dokokin kasar Iran daga shekarar 2008 zuwa 2020.                
      
				
A ranar Lahadin da ta gabata, Iran ta sake gudanar da wasu sabbin canje-canje a kwamitin tsaron kasar, domin yin nazari a kan tsare-tsaren tsaro da kuma karfafa karfin sojin kasar.
Sanarwar da aka fitar a hukumance ta bayyana cewa, shugaba Masoud Pezeshkian ne zai jagoranci kwamitin tsaron, kuma zai hada da shugabannin sassan iko guda uku, wato shugaban kasa, shugaban majalisar dokoki da kuma alkalin alkalai, gami da manyan kwamandojin soji, da ministocin sassan da abin ya shafa.
Majalisar za ta mayar da hankali ne kan tantance dabarun tsaro da kuma inganta karfin soji.
Kafa wannan majalissar ya yi dai-dai da sashe na 176 na kundin tsarin mulkin kasar Iran, wanda ya bai wa kwamitin koli na tsaron kasar damar kirkiro wasu rassa na musamman a lokacin da ya dace don cika bukatun tsaron kasa. Ana sa ran majalisar za ta fara aiki nan ba da dadewa ba, wanda ke nuna wani yunkuri na samar da wasu sabbin dabarun tsaro a daidai lokacin da ake samun ci gaba a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sheikh Qassem: Tsaron Isra’ila zai rushe cikin sa’a 1 idan ta shelanta yaki a kan Lebanon August 6, 2025 Kwamitin Sulhu na MDD ya yi zaman gaggawa kan batun Gaza August 6, 2025 Kamaru: An haramta wa babban dan hamayya tsayawa takara a zaben Oktoba August 6, 2025 Yunkurin Netanyahu na mamaye Gaza ya tayar da balli a Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 6, 2025 Araqch: Hadin Kai Tsakanin Cibiyoyi Na Tabbatar Da Karfi Da Ci Gaba August 5, 2025 Wilayati: Iran Ba Za Ta Amince Da Yin Amfani Da Hanyar Zangezur Ta Hanyar Da Bata Dace Ba August 5, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Da Ke Yankin Jaffa Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 5, 2025 Dr Muhammad Tahir Da Aka Yi Wa Barazanar Kisa Ya Bayyana Abin Da Ya Gani Na Masifa A Gaza August 5, 2025 An Samu Bullar Sabani Da Rikici Tsakanin ‘Yan Sahayoniyya Game Da Batun Mamaye Zirin Gaza August 5, 2025 Jiniyoyin Gargadi Sun Tashi A HKI Bayan Da Yemen Ta Cilla Sabbin Makamai August 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: tsaron kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar
Jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar Kamaru Issa Chiroma Bakary ya kira yi magoya bayansa da su dakatar da dukkanin harkoki domin a tsayar da kasar wuri a matsayin ci gab da nuna kin amincewa da sakamamon zabe.
A can garin Marwa dake a matsayin babban birnin Arewacain kasar,dukkanin harkokin yau da kullum sun tsaya kacokau.
Wani dan kasuwa ya bayyana cewa, rufe kasuwa a wurinsu abu ne mai wahala,amma za su yi ne saboda tsoron kar a kona musu shaguna.
Haka nan kuma ya ce, kasuwar ma ta tsaya cak saboda babu masu saye da suke zuwa.
Da akwai garuruwa da dama da su ka zama kango, saboda kaurewa harkokin yau da kullum da mutane su ka yi a ci gaba da nuna kin yarda da sakamanon zabe.
Wani dan kasuwar mai suna Abdulaziz ya ce; Suna jin tsoron abinda zai faru saboda babu jami’an tsaro da za su ba su kariya.
Wani dalibin jami’a mai suna Gringa Dieudonne ya bayyana cewa gabanin rikicin zabe su 50 ne a cikin ajinsu,amma yanzu su 20 ne kadai suke zama saboda an kauracewa garin.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci